Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD: Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 51 a kudancin Nijar
2020-09-03 09:35:51        cri
Ofishin MDD na tsare tsaren ayyukan jin kai ko OCHA a takaice, ya ce ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake fuskanta tun daga watan Yunin bana a sassan jamhuriyar Nijar, ya haifar da ambaliyar da ta hallaka mutane 51, ta lalata gidaje 26,000, tare da shafar rayuwar al'ummu da yawan su ya kai 281,0000.

Wata sanarwa da ofishin na OCHA ya fitar a jiya Laraba, ta ce ambaliyar ta kuma shafe dubban hektocin filayen noma, lamarin da ka iya haifar da kamfar yabanya a kakar bana.

OCHA ya ce MDD da abokan aikin ta a kasar, na tallafawa gwamnati wajen samar da ababen bukata na yau da kullum, wadanda ba su shafi abinci ba.

Tuni dai MDDr ta rarraba tantunan kwana 4,700 ga masu gudun hijira dake cikin kasar, da ma 'yan kasar da suka kauracewa gidajen su, aikin da ya gudana a birnin Niamey fadar mulkin jamhuriyar ta Nijar, da kuma jihar Diffa dake kudu maso gabashin kasar mai iyaka da Najeriya.

Ofishin OCHA ya ce sama da mutane 72,000 ne suka samu tallafin abinci, da tantuna, da ruwan sha, da kayan kiwon lafiya, da na ba da ilimi, da hidimomin kariya. To sai dai kuma, ofishin ya ce yana bukatar karin kudaden gudanarwa, domin biyan bukatun al'ummun da wannan ibtila'i ya shafa.

Wasu alkaluma sun nuna cewa, a bana kadai, ana bukatar kudi da yawan su ya kai dala miliyan 516 domin cimma wannan buri, ko da yake kawo yanzu, kaso 38 bisa dari kacal ne ofishin na OCHA ya kai ga samu. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China