Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
ICRC:Kimanin mutane 44,000 aka yi rijistar sun bace a Afirka
2020-08-27 10:27:06        cri
Kwamitin ba da agajin jin kai na kasa da kasa na Red Cross (ICRC) ya bayyana a jiya Laraba cewa, ya yi rijista kimanin mutane 44,000 a matsayin wadanda suka bace a sassan nahiyar Afirka, kuma rabi daga cikin wannan adadi kananan yara ne.

Da yake Karin haske cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, kwamitin ya ce kaso 82 na mutanen da suka bace a yankunan na Afirka, sun shafi kasashen Najeriya,da Habasha, da Afirka ta kudu, da Somaliya. Sauran sun hada da Libya ,da Jamhuritar demokiradiyar Congo (DRC) da kasar Kamaru.

Mashawarcin shiyya na kwamitin kan wadanda suka bace da iyalan nasu a Afirka, Sophie Marsac, ya bayyana cewa, rahoton yawan wadanda suka bacen, bai kai ainihin yawan mutanen da iyalansu suke nema ba. Yana mai cewa, tashin hankali, da rikici, da kaurar jama'a da matsalar sauyin yanayi, ba su hana rabuwar iyalai, a lokaci da duniya ke fama da annobar COVID-19 ba, amma a cewarsa, aikin da kwamitin ya ke yi na gano wadanda suka bacen ya kara yin wahala.

A don haka kwamitin na ICRC, ya yi kira ga hukumomi, da su yi la'akari da halin da mutanen da suka bacen ke ciki, da yadda hakan ke tasiri kan iyalansu, su kuma yi amfani da ikonsu, wajen hana aukuwar haka a nan gaba, su kuma dauki matakan gano wadanda suka bace, da sanar da iyalansu makomarsu da ma inda suke.

Najeriya dai ta ba da rahoton kimanin mutane 23,000 da suka bace, wuri mafi yawan mutanen da kwamitin ya samu rahoton bacewar mutane a nahiyar. Sai a watanni shida na farkon wannan shekara ce, kwmitin na ICRC ya samu rahoton sama da mutane 360 da suka bace a kasar ta Najeriya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China