Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Najeriya ya yaba yadda nahiyar Afirka ta yi ban kwana da cutar shan-Inna
2020-08-26 13:53:33        cri
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yaba da yadda nahiyar Afirka ta yi ban kwana da kwayar cutar shan-Inna mai yaduwa a cikin al'umma.

Da yake jawabi yayin taron kwamitin shiyyar Afirka na hukumar WHO karo na 70 ta kafar bidiyo, shugaba Buhari ya bayyana tabbacin cewa, kasashen Afirka za su ga bayan annobar COVID-19, kamar yadda suka ga bayan cutar shan-Inna.

Ya ce, ya tuna lokacin da ya kama aiki a watan Mayun shekarar 2015, Ya yiwa 'yan Najeriya alkawarin cewa, zai kawar da kwayar cutar. A don haka, wannan ya nuna cewa, cika wannan alkawari ba ta 'yan Najeriya ce kadai ba, nasara ce ta al'ummar Afirka baki daya.

Buhari ya bayyana cewa, a yayin da duniya ke yaki da annobar COVID-19, nasarar da nahiyar ta yi ta ganin bayan wannan cuta, ta kara tabbatar da ikirarinsa cewa, idan har aka nuna buri na siyasa, da kara zuba jari da bullo dabaru, kana 'yan kasa suka jajurce, hakika za a rage yaduwar annobar COVID-19.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China