Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutanen da aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Afrika ya kusa miliyan 1.13
2020-08-19 10:18:49        cri

Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Afrika wato Africa CDC ta sanar a ranar Talata cewa, yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a Afrika ya kai 1,128,245, yayin da yawan mutanen da suka mutu ya kai 25,884.

Africa CDC, kwararriyar hukumar lafiyar kungiyar tarayyar Afrika AU, a bayanan da ta fitar na ranar Talata ya nuna cewa, jimillar mutanen da suka warke daga cutar COVID-19 ya kai 846,330 ya zuwa ranar Talata.

A cewar hukumar, kudancin Afrika ne shiyyar da annobar ta fi kamari, sai kuma shiyyoyin arewaci da yammacin Afrika.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China