Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wasu maganganun da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya fada dangane da batun kare muhalli
2020-08-15 16:58:47        cri

"Muhalli mai kyau zai haifar da alfanu da bunkasa tattalin arziki."

Magana ce da Xi Jinping ya fada, yayin da ya yi rangadi a gundumar Anji ta lardin Zhejiang na kasar Sin, a watan Agustan shekarar 2005.

"Muhalli mai kyau wani abu ne da zai amfani kowa cikin daidaito, ba tare da karkata ga wani ba, zai kuma kasance wani babban alfanu ga dukkan jama'a."

Shugaba Xi Jinping ya fadi hakan ne yayin da ya yi rangadi a lardin Hainan na kasar Sin a watan Afrilun shekarar 2013.

"Kasar Sin za ta ci gaba da kokarin sauke nauyin dake bisa wuyanta, inda za ta karfafa hadin gwiwar da take yi tare da sauran kasashe ta fuskar kare muhalli da halittu, ta yadda za mu samu damar gina wani kyakkyawan gida namu, wato duniyarmu."

Kamar yadda shugaba Xi ya fada, cikin wata wasikar taya murna da ya aike wa taron dandalin kasa da kasa na kare muhalli da ya gudana a birnin Guiyang na kasar Sin, a watan Yulin shekarar 2013.

 

Labarai masu Nasaba
Ga Wasu
v Ra'ayin Xi Jinping game da batun matasa 2020-08-12 20:40:33

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China