Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan bindiga sun kashe mutane 8 a Nijar har da Faransawa 6
2020-08-10 10:54:06        cri

Ma'aikatar cikin gida da tsaron al'umma ta jamhuriyar Nijar ta ce, an kashe mutane takwas a ranar Lahadi a yankin Koure, daga cikinsu akwai 'yan kasar Faransa masu yawon shakatawa su shida da 'yan kasar Nijar biyu wato direban motar Faransawan da mai yi musu jagora.

Fadar Elysee Palace ta tabbatar da faruwar lamarin. Ofishin shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, ya fadawa kafar yada labaran kasar Faransa cewa, an kashe 'yan kasar Faransa a ranar Lahadi a jamhuriyar Nijer, kana fadar shugaban ta yi Allah wadai da harin, shugaba Macron ya tattauna ta wayar tarho da shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou game da batun harin.

Mutanen da lamarin ya rutsa da su, sun je ziyara ne don kallon rakumin dawa a yankin Koure mai tazarar kilomita 70 dake kudu maso gabashin birnin Niamey, dake yankin jahar Tillabry, inda aka kai musu hari cikin wata motar hukumar mai zamanta ta kasar Faransa.

Sanarwar da ma'aikatar cikin gidan Nijer ta fitar ta ce, maharan sun budewa motar wuta ne, to sai dai ana ci gaba da gudanar da aikin binciken hadin gwiwa domin gano mutanen dake da hannu wajen shirya harin da kuma tsaurara tsaro a yankin. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China