Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin tana da kilomita duba 36 na layin jirgin kasa mai saurin tafiya ya zuwa watan Yuli
2020-08-09 16:35:21        cri

Hukumar sufurin jiragen kasa ta kasar Sin ta sanar cewa, Sin tana da jimillar layin dogo kilomita 141,400 wanda ya hada yankunan kasar daban daban ya zuwa karshen watan Yuli, daga cikin adadin akwai kilomita 36,000 na layin jirgin kasa mai saurin tafiya.

Kasar ta zuba jarin kudin Sin yuan biliyan 67.1 kwatankwacin dala biliyan 9.67 a fannin sufurin jirgin kasa ya zuwa watan Yuli, wanda ya karu da kashi 3.6 bisa 100 idan an kwatanta da makamancin shekarar da ta gabata, kamar yadda kamfanin kula da sufurin jiragen kasar ta Sin ya wallafa a shafinsa na intanet.

Adadin jarin da aka zuba a manya da matsakaitan ayyukan layin jirgin kasa a kasar ya kai yuan biliyan 49.9 a watan jiya, hakan ya nuna an samu karin kashi 11.3 bisa 100 na makamancin lokacin bara.

A cewar sanarwar, a watanni bakwai na farko, an gina sabbin layukan dogo da ya kai kilomita 1,310 kuma tuni sun fara aiki, wanda ya hada har da layin jirgin kasa mai saurin tafiya kilomita 733. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China