Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bangarori daban-daban na HK sun yi Allah wadai da takunkumin da Amurka ta kakkabawa yankin
2020-08-09 16:29:09        cri

Jiya Asaba, bangarori daban-daban na yankin Hongkong sun bayyana cewa, takunkumin da hukumar kudi ta kasar Amurka ta garkamawa wasu jami'an hukumomin gwamnatin tsakiyar kasar Sin masu aikin dake da alaka da yankin Hong Kong, babu gaskiya a ciki, kuma ba su amincewa da matakin, domin tamkar yin shisshigi ne cikin harkokin cikin gidan kasar Sin. Sun nuna matukar rashin jin dadi tare da yin Allah wadai da hakan.

Kungiyar dimokarat ta raya yankin HK wato DAB ta ba da sanarwa cewa, zargin da gwamnatin Amurka ta yi kan wasu jami'ai ba shi da tushe balle makama. A hakika dai, kowace kasa na da 'yancin kare ikon mulkin kasar da tsaronta da kuma tabbatar da cikakken yankinta, ban da wannan kuma, duk wata kasa a duniya na tsaida dokokinta na kiyaye tsaron kasar. Bangarori daban-daban da jama'ar HK na maraba da dokar tsaron kasar Sin dake da alaka da yankin, kuma sun amince cewa, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin da gwamnatin yankin na da niyyar aiwatar da tsarin "kasa daya mai tafiyar da tsarin mulki iri biyu" cikin dogon lokaci.

Kungiyar masana'antu ta HK ta HKFTU ta ba da wata sanarwar yin Allah wadai da takunkumin da Amurka ta kakkabawa jami'an gwamnatin kasar Sin, da kakkausar murya suna adawa da matakan tsoma baki cikin harkokin kasar Sin da Amurka ta yi.

Darektan sashin 'yan sanda na HK Tang Ping-keung wanda aka shigar da shi cikin jeren sunayen da aka sanya musu takunkumi, ya nuna cewa, yana yin alfahari cewa kiyaye tsaron kasar da ma yankin HK kuma shi ne nauyin dake bisa wuyansa, takunkumin da wata kasa ta ketare ta kakkabawa masa babu amfani gare shi, zai ci gaba da aikinsa yadda ya kamata nan gaba. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China