Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dadin rayuwa a sabon kauyen Daman na jihar Tibet ta kasar Sin
2020-08-08 19:52:44        cri

Kauyen Daman yana gundumar Jilong ta jihar Tibet ta kasar Sin, wanda ya kasance kauye mafi sabunta a kasar Sin.

Kakannin mutanen dake rayuwa a kauyen Daman 'yan asalin kasar Nepal ne, sun dade suna zaune a yankin dake kan iyakar dake tsakanin kasar Sin da Nepal da kuma Indiya, daga baya kakannin mutanen Daman suka kaura zuwa nan, inda suka kasance mutanen da ba su da asalin kasa, ya zuwa shekarar 2003, suka samu damar kasancewa 'yan asalin kasar Sin bisa amincewar majalisar gudanarwar kasar Sin, a shekarar 2004, gwamnatin kasar Sin ta ware kudin Sin yuan miliyan 1.47 domin gina musu gidaje, abun farin ciki shi ne, an kammala aikin gina sabon kauyen Daman mai fadin muraba'in mita 3664, daukacin mutanen Daman sun kaura zuwa sabon kauyen. A shekarar 2011, gidajen kwanansu suka lalace sakamakon girgizar kasa, don haka gwamnatin kasar Sin ta sake ware kudin Sin yuan miliyan 5.64 domin sake gina musu gidaje, a sa'i daya kuma, an raba musu dabbobi da lambun shuka kayan lambu da kayayyakin gida.

Yanzu akwai iyalai 58 dake kumshi mutane kusan 200 a cikin sabon kauyen nan, kuma matsakaicin kudin shigar kowanensu ya kai kudin Sin yuan dubu 12 a ko wace shekara, kana daukacin yara sun shiga makaranta, mutanen kauyen Daman suna jin dadin rayuwa matuka.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China