Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tawagar gwajin kwayar cutar COVID-19 ta babban yankin kasar Sin ta fara aiki a HK
2020-08-08 16:59:18        cri

A jiya Jumm'a kakakin gwamnatin Hong Kong, yankin musamman na kasar Sin ya bayyana cewa, tawagar majinyata da gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta tura domin taimakawa yankin game da gwajin kwayar cutar numfashi ta COVID-19 bisa bukatar gwamnatin yankin, ta riga ta fara aiki.

Kakakin ya kara da cewa, tawagar gwajin ta yankin Hong Kong da tawagar gwaji da gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta tura yankin, sun kira taron aiki jiya, inda suka tattauna kan batutuwan da suka shafi yadda za su gudanar da aikin gwajin kwayar cutar a yankin a nan gaba.

Kana tawagar majinyata masu kwarewar aikin asibitin wucin gadi da gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta tura yankin Hong Kong, za ta gabatar da shawarwari da kayayyakin kiwon lafiya ga yankin.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China