Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabar UNECA ta bukaci a bunkasa kasuwanci tsakanin kasashen Afrika domin bunkasuwar kasuwancin kasa da kasa
2020-08-07 09:36:25        cri
Babbar sakatariyar hukumar raya tattalin arzikin Afrika ta MDD, ECA, Vera Songwe, ta jaddada bukatar bunkasa harkokin kasuwanci a tsakanin kasashen Afrika da nufin samar da gudunmawa daga bangaren Afrika wajen bunkasuwar kasuwancin duniya.

Jami'ar hukumar ECA, ta yi wannan kira ne a lokacin tattaunawa ta kafar bidiyo game da matsayar Afrika kan batun kungiyar kasuwanci ta duniya WTO da kuma makomar shiyyar game da hadin gwiwar cinikayya, inda ta jaddada bukatar bunkasa harkokin kasuwanci a tsakanin kasashen Afrika.

Hada hadar kasuwancin Afrika a tsakanin kasashen duniya ya kai kashi biyu bisa 100 a shekaru 20 da suka gabata. Har yanzu adadin yana a matakin kashi 2 bisa 100 ne duk da kasancewar shiyyar ta shiga kungiyar WTO kuma akwai kasashe masu yawa wadanda suke huldar cinikayya a wajen nahiyar, inji Songwe.

A cewar Songwe, yayin da Afrika take kasuwanci a tsakanin shiyyar, zata kara samun daraja, kuma idan ta samu karin daraja, zata kara samun arziki da raguwar talauci.

Songwe tace, kasashen Afrika suna magana da murya guda game da batun cinikayya kuma suna kokarin daidaita batun ta hanyar aiwatar da yarjejeniyar kasuwanci ta AfCFTA.

A cewar hukumar ECA, idan har ta fara gudanar da aikinta, yarjejeniyar zata iya bunkasa kasuwanci tsakanin kasashen Afrika da karin sama da kashi 52 bisa 100 nan da shekarar 2022. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China