Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bunkasuwar kauyen Dalishu dake lardin Liaoning na kasar Sin
2020-08-06 16:30:38        cri

A birnin Fengcheng na lardin Liaoning dake arewa maso gabashin kasar Sin, akwai wani kauye mai suna Dalishu, inda aka kafa wani dakin nune-nunen ayyukan gona na zamani.

A halin yanzu, ta hanyar amfani da fasahohin zamani, masu kula da dakin suna amfani da na'ura mai kwakwalwa kawai domin daidaita yanayin da ake ciki. Alal misali, ana bukatar ma'aikata sama da 20 a cikin wani dakin noma mai fadin murabba'in mita 12000, amma a nan, ana bukatar guda 8 kacal.

A shekaru sama da 30 da suka shige, mazauna kauyen Dalishu sun yi fama da kangin talauci, amma sakamakon matukar kokarin da suka yi, kauyen ya zama abun misali a fannin yawon bude ido a kasar Sin. A shekara ta 2019, jimillar darajar kayayyakin da aka samar baki daya a kauyen ya kai Yuan biliyan 1.6, kuma jimillar dukiyoyin kauyen ya zarce Yuan miliyan 600, sa'annan matsakaicin kudin shiga da kowane mazaunin kauyen ya samu ya kai Yuan 22000 a kowace shekara.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China