Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wani masanin Amurka ya soki lamirin Pompeo da sauran 'yan siyasar kasar
2020-08-06 14:21:52        cri

Babban manazarci a jami'ar Yale ta Amurka, Stephen S.Roach ya bayyana ta kafar CNN cewa, wasu jami'an gwamnatin kasar guda hudu, ciki hadda sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo, sun wallafa wasu dogayen bayanai a cikin wata guda da ya gabata, wadanda suka shafi kasar Sin. Amma a cewar Mista Roach, wadannan bayanan cike suke da ra'ayoyin dake bata sunan kasar Sin, kuma ba su da tushe balle makama.

Roach ya ce, jami'an hudu masana ne a fannin doka, amma ba su da ilimi da kwarewa sosai a fannin tattalin arziki.

A cewarsa, bata sunan wata kasa, wata dabara ce da gwamnatin Trump take son amfani da ita a kowane lokaci. Shi ma Pompeo yana amfani da ita kan batun da ya shafi kasar Sin. Yayin da suke yunkurin shafawa kasar Sin bakin fenti, wadannan jami'an gwamnatin Amurka sun bayyana ra'ayoyin ne da nufin cimma muradunsu na siyasa.

Roach ya ce, tabarbarewar alakar Sin da Amurka za ta haifar da rashin tabbas ga tattalin arzikin Amurka.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China