Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kungiyoyi masu rajin kare muhalli a Afirka sun kaddamar da gangamin karfafa yaki da cutukan da dabbobi ke yadawa
2020-08-06 11:28:30        cri
Gungun kungiyoyi masu rajin kare muhalli a nahiyar Afirka, sun kaddamar da wani gangamin wayar da kai, da karfafa yaki da cutukan da dabbobi ke yadawa bil Adama.

Gamayyar kungiyoyin daga kasashen dake kudu da hamadar sahara, sun kaddamar da gangamin nasu ne a ranar Laraba, da nufin karfafa yaki da irin wadannan cututtuka, ta hanyar kare muhallin halittu yadda ya kamata.

Rahotanni sun ce, gangamin ya samu goyon bayan kungiyoyi mahalarta 80 dake rajin kare muhallin halittu, wadanda suka sha alwashin wayar da kan al'ummu tun daga matakin farko, ta yadda za a fahimci tasirin kula da muhallin halittu, a fannin yaki da cutukan da dabbobi ke yadawa bil Adama.

Da yake karin haske kan wannan gangami, babban shugaban cibiyar kare gandun daji ta AWF dake birnin Nairobin kasar Kenya Mr. Kaddu Sebunya, ya ce "A matsayin mu na masu rajin kare muhallin halittu, muna kan gaba wajen ba da gudummawa, ga yakin da ake yi da cutukan da dabbobi ke yadawa bil Adama.

Mr. Sebunya ya kara da cewa, gamayyar ta su, ta samar da wani dandali, na tattauna kalubalen da nahiyar Afirka ke fuskanta a cikin gida, tare da bankado damammaki da za su daga muryar nahiyar, da baiwa albarkatun ta kariya, da ma batun kare lafiyar al'ummun nahiyar.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China