Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana inganta kwaskwarimar kamfanoni mallakar gwamnati a birnin Shenyang
2020-08-05 11:31:33        cri

Akwai kamfanoni mallakar gwamnati da dama a lardin Liaoning na kasar Sin. Cikin 'yan shekarun nan, lardin Liaoning yana mai da hankali matuka kan aikin kwaskwarima ga irin wadannan kamfanoni, domin karfafa bunkasuwar lardin.

Bisa kokarin da aka yi, ya zuwa yanzu, an cimma sakamako da dama, musamman a fannin kwadago da tsarin raya kananan kamfanoni, inda wasu ma'aikatan kamfanoni mallakar gwamnati, suka kafa kamfanoni mallakar kansu.

Ma Di, ya taba aiki a wani kamfanin sarrafa na'urori mallakar gwamnati a birnin Shenyang, fadar mulkin lardin Liaoning. Sa'an nan a shekarar 2018, kamfaninsa ya kafa shirin sa kaimi ga ma'aikata da su kafa kananan kamfanoni. Ma Di daya ne daga cikin wadanda suka shiga wannan tsari.

Ya ce, wannan kyakkyawar dama ce gare shi, ko da yake, akwai karin ayyuka da kuma karin nauyin da ya kamata ya sauke, amma, zai iya samun karin kudaden shiga bisa kokarinsa. Kana, tsohon kamfaninsa ya samar da wurare, da na'urori, da taimakon da yake bukata gare shi, da kuma tsarin raba ribar da suka samu cikin hadin gwiwa.

Daga ma'aikacin kamfani mallakar gwamnati, zuwa shugaba na kamfanin kashin kansa, Ma Di ya fara kula da harkokin kasuwanni da kansa, ya kuma canja halin da yake ciki a fannin ayyuka da ma zaman rayuwa.

Ya ce, "na gamsu sosai, sabo da akwai odoji da dama, lamarin da ya sa, kamfanina ke samun ci gaba. Har kudin shiga da nake samu suka ninka, yanzu, ina zaman rayuwa cikin matsakaiciyar wadata!" (Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China