Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta bukaci Amurka ta yi cikakken bayani kan aikin soja na gwajin halittu da ta yi a kasashen waje
2020-08-05 10:43:56        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a jiya Talata a birnin Beijing cewa, kasar Amurka tana gudanar da aikin soja na gwajin halittu a asirce, ba kuma tare da daukar matakan kare tsaro ba a kasashen ketare da dama, don haka Sin ke kira ga Amurkan da ta yi cikakken bayani kan irin wadannan ayyukan soja da take yi.

Wang Wenbin ya ce, kasar Amurka tana gudanar da aikin soja na gwajin halittu a kasashe da dama, da farko tana yin hakan a asirce, ta yadda wasu daga kasashe ba su ma san yaya aikin gwajin halittun da kasar Amurka ke gudana a kasashensu ba.

Kaza lika, a matsayin kasar da ta fi gudanar da ayyukan gwajin halittu, Amurka ba ta taba ambatar wannan aiki cikin yarjejeniyar hana makamai na halittu ba. Sa'an nan kuma, rundunar sojojin kasar Amurkan tana gudanar da aikin gwajin halittun ba tare da daukar matakan magance hadurra ba.

Jami'in ya ce wasu ayyukan gwajin da kasar Amurka ke yi, suna da nasaba da kwayoyin cuta masu hadari, ta yadda idan ta gamu da matsala a lokacin da ake gwajin halittu, mai iyuwa ne hakan ya haddasa babbar illa ga kasar da ake aikin a cikin ta, da ma kasashen dake kewayenta, har ma duk duniya baki daya.

Haka kuma, gwajin da rundunar sojan kasar Amurka ke yi, bai dace da ka'idojin kasa da kasa ba. Sabo da a halin yanzu, kasar Amurka ce kasa daya tak da ta kafa dakunan gwajin halittu cikin kasashe daban daban, tana kuma kwashe albarkatun halittun kasashen ketare, kuma, ita kadai ta ki amincewa da shawarwari kan yarjejeniyar hana makamai na halittu.

Wang Wenbin ya jaddada cewa, kasar Sin tana fatan kasar Amurka ta yi cikakken bayani kan gwajin halittu da take yi a kasashen ketare, bisa ka'idojin ba tare da boye komai ba, da sauke nauyinta yadda ya kamata, domin amsa bukatun kasa da kasa. Kuma, ya kamata ta aiwatar da yarjejeniyar hana makamai na halittu yadda ya kamata, ta kuma dakatar da matakinta na hana yin shawarwari kan yarjejeniyar. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China