Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta ci gaba da bude kofa ga ketare domin kara hadin gwiwa tsakaninta da sauran kasashe
2020-08-04 21:03:21        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a yayin taron ganawa da manema labarai a nan birnin Beijing yau cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kara habaka bude kofa ga ketare domin kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da sauran kasashen duniya, ta yadda za su samu moriya tare.

Rahotanni sun nuna cewa, kwanan baya wasu 'yan siyasa kalilan sun yi shelan cewa, kamfanonin ketare za su bar kasar Sin, kan wannan batun, jami'i Wang Wenbin ya mayar da martini, kuma ya gabatar da sabbin alkaluman da aka fitar, inda ya bayyana cewa, "Tun bayan barkewar annobar COVID-19, kasar Sin ta yi nasarar hana yaduwarta kafin sauran kasashen duniya, har ta yi nasarar farfado da tattalin arziki a kasar daga duk fannoni, kana alkaluman da hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, tattalin arzikin kasar ya karu da kaso 3.2 cikin dari a rubu'i na biyu na bana, a don haka ba zai yiyu ba kamfanonin jarin waje da dama su bar kasuwar kasar ba."

Kana Wang Wenbin ya kara da cewa, yanzu haka kamfanonin ketare da dama suna kara himmatuwa wajen gudanar da harkokinsu a kasar Sin, saboda yanayin kasuwanci da kasuwanni na kasar suna kara kyautuwa.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China