Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kammala aikin hajjin bana yayin da ake tsaka da fama da annobar COVID-19
2020-08-04 10:52:17        cri
Hukumomin lafiya na Saudiyya, sun ce ba a samu rahoton wanda ya kamu da cutar COVID-19 ba yayin aikin hajjin bana.

A jiya Litinin ne mahajjata suka yi wa garin Makkah ban kwana, bayan sun kammala aikin hajjin.

Majalisar kula da harkokin ka'abah da masallacin Annabi, sun samar da dukkan abubuwan da ake bukata ga mahajjatan yayin da suke kuma tabbatar da daukar matakan kandagarki daga annobar.

Masarautar Saudiyya ta shirya hajjin bana da kayyadaddun mahajjata saboda annobar COVID-19, inda a mahajjatan sun kasance mazauna kasar kadai.

A jiya Litinin, hukumar lafiya ta kasar ta sanar da sabbin mutane 1,258 sun kamu da COVID-19, wanda ya kawo jimilar masu cutar zuwa 280,093.

Har ila yau, baki daya adadin wadanda suka warke ya karu zuwa 242,053, inda aka samu sabbin mutanen da suka warke 1,972. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China