Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Launin wurin rairayi dake cikin hamadar Mu Us ta canja zuwa kore
2020-08-02 21:02:25        cri

Hamadar Mu Us mai fadin muraba'in kilomita dubu 42.2 tana sauka ne a yankin Wushen na birnin Ordos na jihar Mongolia ta gida ta kasar Sin, tun daga shekarun 1960, mazauna wurin sun fara dasa itatuwa a kan rairayi, domin kyautata muhalli, kawo yanzu, launin wurin yana canzawa zuwa launin kore a kai a kai.

Ubana ya ce: "Maza maza ka dawo, kusan ban iya bude kofa ba saboda rairayi."

Bapa Jirigalatu ya zauna a cikin gidansa irin na zamani da aka gina a kan filin ciyayi, ya waiwayi yanayin da iyalinsa ke ciki kafin shekaru sama da 30 da suka gabata inda ya bayyana cewa, a wancan lokaci, babu ciyayi da yawa a kusa da gidansa, ko ina rairayi ne kawai, iyalinsa tana kiwon tumaki goma da saniya guda daya kacal a filin.

Bapa Jirigalatu da matarsa sun koma garinsu ne bisa bukatar ubansu, kuma sun tsaida kuduri cewa, za su yi kokarin dasa itatuwa a kan rairayi domin sauya launin wurin zuwa kore.

Amma akwai wahala su cimma burin nasu, saboda ba su san yadda ake dasa itatuwa a kan rairayi ba, har itatuwan da suka dasa ba su girma ba a cikin farkon shekaru biyar.

Ya zuwa shekara ta biyar, sun yi nasarar dasa itatuwa a kan rairayi.

Bapa Jirigalatu ya gaya mana cewa, a shekarar 2005, ya dasa itatuwa a duk fadin filin rairayin iyalinsa.

Yanzu dai iyalinsa suna kiwon tumaki sama da 200 da shanu sama da 40, adadin kudin shigarsu a duk shekara ya kai kudin Sin yuan fiye da dubu 180, abun farin ciki shi ne suna zaman rayuwa ne a cikin sabon gida irin na zamani.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China