Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shigar da Sin kara kan cutar COVID-19 babban kuskure ne, in ji 'yar majalisar dattijan Amurka
2020-08-02 17:05:45        cri

Wata 'yar majalisar dattijai a jihar California ta Amurka ta ce, baiwa Amurkawa damar shigar da karar kasar Sin game da batun annobar COVID-19 babban kuskure ne.

'Yar majalisar dattijai Dianne Feinstein, ta ce sun gabatar da jerin al'amurra masu yawa wadanda ba'a san su ba wadanda ke cike da matukar hadari. Don haka tana ganin wannan babban kuskure ne. Sanatar ta bayyana hakan ne a kwanan nan a lokacin sauraron taron kwamitin kula da harkokin shari'a na majalisar dattijan Amurka.

Ta bayyana cewa, kasar Sin ta fidda miliyoyin mutane daga kangin talauci a cikin kankanin lokaci, Feinstein ta bayyana Sin a matsayin wata kasa dake samun bunkasuwar daraja da kima a idanun sauran kasashen duniya kuma tana neman zama babbar abokiyar huldar cinikayya.

Feinstein ta kara da cewa, sauran kasashen duniya, ciki har da kasar ta Sin, za su iya amfani da sabon tsarin shari'a wajen kalubalantar Amurka, lamarin da zai iya haifar da rikici a duniya, kamar yadda kafar yada labarai ta Fox News ta bayyana.

Sharhin da ta gabatar ya zo ne watanni uku bayan da babban mai shari'a na jihar Missouri, Eric Schmitt ya shigar da kara inda ya bukaci gwamnatin kasar Sin ta dauki alhaki kuma ta biya diyyar annobar da ta barke a duniya.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China