Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin masu COVID-19 a nahiyar Afrika ya zarce 900,000
2020-08-01 16:37:23        cri
Cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta Africa CDC, ta ce adadin wanda aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a fadin nahiyar Afrika ya kai 908,931.

Cibiyar Africa CDC ta bayyana cikin rahotonta na jiya Juma'a cewa, adadin ya karu daga 891,199 a ranar Alhamis, zuwa 908, 931 zuwa jiya, wanda ke nufin an samu karuwar mutum 17,732 a dan tsakanin.

Ta kara da cewa, adadin wadanda cutar ta yi ajalinsu ma ya karu daga 18,884 a ranar Alhamis, zuwa 19,310 a jiyan.

Har ila yau, cibiyar ta jaddada cewa, kawo yanzu, mutane 556,695 da aka tabbatar sun kamu da cutar a fadin nahiyar, sun riga sun warke.

Kasar Afirka ta kudu ita ce ke kan gaba da yawan masu cutar, inda adadinsu ya kai 482,169, sai kasashen Masar da Nijeriya da Aljeria da Morocco dake rufa mata baya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China