Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Chen Wei, manjon janar kasar Sin "mai kawo karshen kwayoyin cuta"
2020-08-01 16:32:31        cri

An yi wa Chen Wei allurar yaki da cututtuka kafin ta tafi birnin Wuhan na kasar Sin

Chen Wei, masaniya mai nazarin cututtuka masu yaduwa na kasar, kana wata manjon-janar ce ta rundunar sojojin kasar Sin. A shekarar 2003, ta tafi asibitocin musamman na jinyar masu cutar SARS guda 83 a wurare daban daban na kasar Sin, inda ta taka muhimmiyar rawa wajen nazarin magungunan yaki da cutar SARS. A shekarar 2014, ita da tawagarta sun cimma nasarar gwajin allurar rigakafin cutar Ebola a yankin yammacin Afirka, don haka mazauna yankin suka kira ta da sunan "mai kawo karshen kwayoyin cuta". A shekarar 2020, ta jagoranci tawagar nazarin kimiyya da fasaha don yin nazarin allurar rigakafin cutar COVID-19, yanzu an shiga matakin gwajin allurar a asibiti a hukunce, hakan ya kawo kyakkyawan fatan kawo karshen cutar.

"Yanayin tinkarar cututtuka yanayi ne da sojojin ke tinkara, yankuna masu fama da cututtuka yankuna ne da sojojin ke kula da su," a cewarta. Kana ta ce ya kamata a yi kokarin gudanar da dukkan ayyukan da aka baiwa mata, domin ta sanya rigar soja. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China