Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tawagogin likitoci na sojojin kiyaye zaman lafiya da kasar Sin ta tura wa Afirka sun ba da gudummawar yaki da cutar Ebola
2020-08-01 16:32:24        cri
Cutar Ebola daya daga cikin cututtuka masu yaduwa da suka fi haddasa rasuwar mutane a duniya. Cutar Ebola ta barke a nahiyar Afirka a shekarar 2014, kuma kasar Liberia kasa ce da ta fi fama da yaduwar cutar, a lokacin, sojojin kiyaye zaman lafiyar kasar Sin dake wurin sun dukufa wajen aiwatar da ayyukansu yadda ya kamata, da kuma kare manyan hanyoyin mota guda uku na kasar.

Sa'an nan, a karshen shekarar 2018, cutar Ebola ta sake barkewa a nahiyar Afirka, tawagar likitoci na sojojin kiyaye zaman lafiya da kasar Sin ta tura wa kasar Congo-Kinshasa, sun tafi wurare da dama sun yi aikin ceton jama'ar kasar, lamarin ya samu yabo matuka daga kungiyar sojojin kiyaye zaman lafiya ta MDD dake kasar Congo-Kinshasa. (Maryam Yang)

Hoto: A asibitin zumunci na Sin da Saliyo dake kasar Saliyo, wani likitan sojan Sin yana sufurin samfuran kwayoyin cutar Ebola.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China