Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya sanar da kaddamar da tsarin shawagin tauraron dan-Adam na BeiDou-3 a hukumance
2020-07-31 13:43:22        cri

Yau Jumma'a da safe, an yi bikin kammala kaddamar da tsarin shawagin tauraron dan-Adam na BeiDou-3 a birnin Beijing. Babban sakataren kwamitin tsakiyar Jam'iyyar Kwaminis ta Sin, shugaban kasa, kana shugaban rundunar sojojin kasar Xi Jinping ya halarci bikin, inda ya sanar da kaddamar da tsarin shawagin tauraron dan-Adam na BeiDou-3 a hukumance.

Bayan Xi Jinping ya sanar da hakan, aka fara amfani da wannan tsarin shawagin tauraron dan-Adam na BeiDou-3 kirar kasar Sin, wanda ya zama muhimmin bangare cikin ababen more rayuwa da aka gina cikin sararin samaniya.

Cikin bikin da aka yi a yau, wakilin ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar JKS, kana mataimakin shugaban rundunar sojojin kasar Sin, Zhang Youxia ya karanta sakwannin taya murna daga kwamitin tsakiyar JKS, da majalisar gudanarwar Sin, da rundunar sojojin kasar, inda suka yaba matuka dangane da kammala wannan muhimmin aiki. Sakwanninsu sun nuna cewa, kaddamar da tsarin ya nuna muhimmiyar rawa da kasar Sin ta taka a fannin kimiyya da fasahar jiragen sama, kana ya zama muhimmiyar gudummawar da kasar Sin ta ba kasa da kasa a fannin ginin ababen more rayuwa, kuma shi ne babban sakamakon da kasar Sin ta cimma bayan ta shiga sabon zamani. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China