Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta yabawa Sin kan yadda take taimakawa Afirka kara karfinta na yaki da cututtuka
2020-07-30 09:10:26        cri

Kungiyar tarayyar Afirka (AU) ta yabawa kasar Sin, kan yadda take ci gaba da goyon baya da ma taimaka mata wajen kara karfin nahiyar kan yaki da kandagarki da hana yaduwar cututtuka.

Wata sanarwa da kasashe mambobin kungiyar 55 suka fitar jiya Laraba, ta bayyana cewa, kungiyar ta sanya hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da kasar Sin, yayin bikin aikin gina kashin farko na hedkwatar cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Afirka (Africa CDC).

Kwamishinar kula da jin dadin jama'a ta kungiyar, Amira Elfadil da mataimakin ministan cinikayya na kasar Sin Qian Keming ne suka sanya hannu a kan aikin gina hedkwatar Africa CDC da ya gudana ta kafar bidiyo a madadin sassan biyu.

A jawabinta, Amira Elfadil, ta yabawa gwamnatin kasar Sin, kan yadda take taimakawa Afirka kara karfinta na kandagarki da hana yaduwar cututtuka a nahiyar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China