Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bankin duniya: AFCFTA za ta taimakawa Afirka samun kudin shigar da ta kai dala biliyan 450
2020-07-29 09:44:09        cri

Wani rahoto da bankin duniya ya fitar Litinin din da ta gabata, ya bayyana cewa, idan har aka aiwatar da yarjejeniyar cinikayya maras shinge ta Afirka ko AfCFTA a takaice yadda ya kamata, hakika, nahiyar za ta iya samun kudin shigar da ya kai dala biliyan 450.

A cewar rahoton, yarjejeniyar za kuma ta bunkasa cinikayyar nahiyar, musamman cinikayyar kayayyakin masana'antu tsakanin kasashen nahiyar. Rahoton ya kara da cewa, daga cikin dala biliyan 450 din da nahiyar za ta samu daga AfCFTA, dala biliyan 292 zai fito ne daga cikakken cinikayya, matakan da za su rage wasu ka'idoji da kananan matakai na kwastam.

An dai tsara rahoton ne, don yiwa masu tsara manufofi jagora, yayin da suke ci gaba da sasantawa da ma aiwatar da wannan yarjejeniya. Binciken da aka gudanar ya ba da shawarar cewa, cimma wannan buri abu ne mai muhimmanci, idan aka yi la'akari da illar da cutar COVID-19 ta yiwa tattalin arziki, wanda ake sa ran zai haifarwa nahiyar Afirka hasarar da ta kai dala biliyan 79 a shekarar 2020 da muke ciki. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China