Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masu rajin kare halittu a Afrika sun koka dangane da karuwar barazana kan giwaye da damisar Cheetah
2020-07-27 11:04:58        cri

Masu rajin kare dabbobi a Afrika, sun yi kira ga abokan huldarsu da gwamnatoci, da su dauki matakai dangane da karuwar barazana ga giwaye da damisar Cheetah, wadanda suka hada da cututtuka da hadarin dabbobi ga dan Adam da kuma fari da ake samu akai akai.

Winnie Kiiru, babbar mai bada shawar ga shirin kare giwaye na EPI, ta ce dabbobin masu daraja na fuskantar sabbin barazana daga muhalli da dan Adam, don haka, akwai bukatar kara inganta kokarin ba su kariya.

Ta ce annobar COVID-19 ta yi mummunar illa kan kare giwaye a Afrika, baya ga raguwar kudin da ake samu daga yawon bude ido.

A cewarta, ya kamata gwamnatocin Afrika sun lalubo hanyoyin da za su farfado da shirye-shiryen kare giwaye da damisar Cheetah, yayin da ake fuskantar hadarin safararsu ba bisa ka'ida ba da kuma raguwar muhallinsu saboda karuwar al'umma.

Kiddidiga daga asusun kare dabbobin daji na duniya WWF, ta nuna cewa, yawan giwayen Afrika ya tsaya kan 415,000 a 2019, yayin da kusan 15,000 ke mutuwa duk shekara saboda safararsu da ake yi da kuma wasu iftila'i indallahi. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China