Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Daidaituwar Star Market ta taka rawa ga fannin kirkire-kirkire da ci gaban kasar Sin
2020-07-22 20:32:42        cri

A yau ne hukumar fasahar kirkire-kirkire (Star Market) wadda aka fi sani da kasuwar yiwa hannayen jari gyaran fuska na gwaji ta kasar Sin, ke bikin cika shekara guda ta kafuwa. A cikin shekarar da ta gabata ce, aka aiwatar da tsarin yin rijistar hukumar ba tare da wata tangarda ba, kuma kirkire-kirkire a muhimman tsare-tsare da aka yi sun dace da yanayi na kasuwa.

Bugu da kari, an cimma muhimman nasarori wajen taimakawa kimiya da fasahar kirkire-kirkire, da bunkasa yadda ake farfadowa da daga matsayin tattalin arzikin kasar Sin da sanya sabbin dabaru wajen raya tattalin arzikin duniya.

Yanzu haka tattalin arzikin kasar Sin ya shiga wani muhimmin lokaci na sauya tsoffin tsarin bunkasuwa da sabbi, a don haka akwai bukatar bunkasa sabbin fasahohi da masana'antu. A ranar Talata ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada bukatar kara zage damtse wajen bunkasa kimiya da fasahar kirkire-kirkire, da hanzarta warware muhimman matsaloli da bangaren fasahohi ke fama da su, da kirkiro sabbin dabarun raya makoma. A wannan shekara ce, kasuwar hannayen jarin kasar Sin ke cika shekaru 30 da kafuwa. Kuma a saboda muhimman gyare-gyare da aka gudanar, ya taimakawa ga dorewar kasuwar hannayen jarin kasar ta Sin. Ana kuma fatan cewa, daidaituwar kimiyar kirkire-kirkire, ba kawai za ta bunkasa yiwa kasuwar hannayen jarin kasar da ci gaban tattalin arziki mai salon kirkire-kirkire ba, har ma zai taimakawa tattalin arzikin duniya fita daga halin da yake cikin nan da nan. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China