Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Karuwar adadin masu cutar COVID-19 a Afrika ta kudu babban hadari ne ga nahiyar Afrika baki daya
2020-07-21 16:41:14        cri

Ya zuwa jiya Litinin, kasar Afrika ta kudu ta bada rahoton samun mutane 364,328 da suka harbu da cutar COVID-19.

Karuwar wannan adadi ya zama abun damuwa, musamman ga al'ummar Afrika da kuma hukumar lafiya ta duniya, bisa la'akari da cewa, adadin na iya zama alamun dake nuna cewa cutar za ta kara kamari a fadin nahiyar.

Lallai tsugune ba ta kare ba. Kamar dai yadda sakatare-janar na hukumar lafiyar ke ta nanata gargadi, yana cewa, ko kusa, annobar COVID-19 ba ta yi da zuwa karshe ba.

A cewar cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta Afrika, jimillar wadanda suka kamu da cutar a fadin nahiyar, ya karu daga 683,905 da yammacin ranar Asabar zuwa 701,573 ya zuwa safiyar ranar Lahadi. Haka zalika, adadin wadanda cutar ta yi ajalinsu, shi ma ya karu, zuwa 14,937. Baki dayan adadin masu cutar a nahiyar bai kai na Amurka ba, sai dai karuwar da aka samu a Afrika ta kudu, ya sa kasar ta zama ta 5 a duniya, cikin jerin kasashen da cutar ta fi kamari.

A cewar kiddidigar jami'ar Johns Hopkins, cikin mako guda, an samu karuwar masu kamuwa da cutar da kaso 30 cikin 100.

Wannan ya zama abun tsaro da tashin hankali ga nahiyar Afrika, musamman a lokacin da gwamnatocin nahiyar ke ci gaba da sassauta matakan da suka dauka na kandagarki da dakile cutar.

Yayin wani taron manema labarai a jiya Litinin a Geneva, Daraktan sashen shirye-shiryen matakan gagagwa na hukumar lafiya ta duniya Dr. Mike Ryan, ya ce yayin da Afrika ta Kudu ke fuskantar yanayi mai tsanani, a ganinsa, alamu ne na abun da nahiyar ka iya fuskanta, idan har ba a gaggauta daukar mataki tare da samar da karin taimako ba.

Ya ce a wani lokaci, cutar kan yadu cikin sauri, sannan a wani lokaci, ta fara yaduwa a hankali, kafin daga bisani ta tsananta, kuma fahimtar dalilin hakan, abu ne mai wahala.

Baya ga Afrika ta kudu, an samu karuwar cutar a kasashen Namibia da Botswana da Madagascar. Lallai wannan sabon yanayi ya zama abun da ke kira ga kasashen nahiyar su farga, su kara daura damarar yaki da cutar. Bai kamata su yi sakaci da wannan batu ba, domin ya samar musu da lokaci da dama na tunkarar abun da iya zuwar musu.

Akwai bukatar kasashen nahiyar su nazarci yanayinsu da kuma halin da su da baki dayan nahiyar ke ciki, kafin saurin sassauta matakansu, don kada su zama 'yan a bi yarima a sha kida.

Sassauta matakai masu inganci da suka dauka, har ake yaba musu, ka iya zama koma baya idan har ba a samu nasarar shawo kan cutar a nahiyar baki daya ba. Abun da ya kamata su yi shi ne, kara nazari da hadin kai, don lalubo dabarar da za ta yi musu amfani a lokaci guda. Wato su hada kai wajen lalubo hanyar dakile cutar cikin kasashensu da kuma tabbatar da rashin yaduwarta a tsakaninsu, ta hanyar aiwatar da dabara a lokaci guda, domin su gudu tare su tsira tare. (Faeza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China