Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
COVID-19: Neman diyyar farfesa Azinge daga kasar Sin tamkar wuce gona da iri ne
2020-07-20 16:17:20        cri

A karshen makon da ya gabata ne jaridar Sun News ta intanet ta wallafa wani bayani game da yunkurin wani lauya daga Najeriya farfesa Epiphany Azinge, wanda ya jagoranci wata tawagar kwararrun lauyoyi don shigar da kara inda suka bukaci kasar Sin ta biya zunzurutun kudi har dala biliyan 200 ga Najeriya, bisa hujjar da suka bayyana cewa wai kasar Sin ta yi sakaci game da barkewar annobar COVID-19 lamarin da ya haifarwa Najeriya hasarar rayuka, da tabarbarewar tattalin arziki, da katsewar hada hadar yau da kullum ga jama'ar kasar. Koda yake, farfesa Azinge ya ambata cewa ya dauki wannan mataki ne bisa ra'ayin kansa. To amma, a bisa dukkan alamu matakin nasa zai iya zama abin da masu hikimar magana ke cewa "wuce makadi da rawa" ko kuma a wani kaulin, za'a iya bayyana shi da cewa "riga malam masallaci". Wannan mataki tamkar wuce gona da iri ne, domin kuwa ya dauki matakin ne bisa ra'ayinsa na kashin kai, ba tare da yawun mahukuntan Najeriya ba. Koda yake, daga cikin dalilan da masanin shari'ar ya bayyana a matsayin hujjojinsa na shigar da wannan kara, ya yi zargin cewa, hukumomin lafiyar kasar Sin, da cibiyar nazarin kimiyyar kasar, da cibiyar dakile cutuka masu yaduwa ta kasar Sin, gami da cibiyar nazarin kwayoyin cutuka ta Wuhan sun yi sakaci wajen gaza daukar matakai a kan kari domin sanar da hukumar lafiya ta duniya WHO lokaci yayin da aka samu barkewar cutar ta COVID-19. Wata kila farfesan Azinge bai lura da irin matakai da hukumomin kasar Sin ke dauka ba tun daga lokacin da aka samu barkewar wannan annobar. A lokuta da dama mahukuntan kasar Sin sun sha nanata aniyar kasar na yin hadin gwiwa da kasa da kasa domin nazarin kan annobar COVID-19 har ma da tushen cutar. Har zuwa wannan lokacin kwararrun masanan kasa da kasa ba su kai ga yanke hukuncin karshe game da tushen annobar COVID-19 ba. Alal misali, ko a farkon wannan wata na Yuli, wata tawagar masu bincike daga jami'ar tarayya ta Santa Catarina ta Brazil ta ce, daga watan Oktoban bara zuwa Maris na bana, ta gudanar da bincike kan samfuran ruwan masai a Florianopolis, babban birnin jihar Santa Catarina ta kasar, inda a watan Nuwamban bara ta gano cewa, akwai kwayoyin cutar Corona a ruwan masan. Wannan ya zo ne watanni 2 kafin sanar da samun mutum na farko da aka tabbatar ya kamu da cutar a hukumance a nahiyar Amurka, haka kuma, watanni 3 kafin gwamnatin Brazil ta sanar da samun bullar cutar a kasar, a karshen watan Fabrerun bana. Wannan bincike ya zama karin shaida mai karfi dake nuna cewa, an dade da samun cutar a kasashe da dama. Haka ma lamarin yake a jami'ar Barcelona ta Spaniya, inda ta ce masu bincike a jami'ar sun gwada samfuran ruwan masai kuma sun gano akwai birbishin kwayar cutar COVID-19 a ruwan da suka tattara a ranar 12 ga watan Maris na shekarar 2019, amma Spaniya ba ta bada rahoton bullar cutar na farko ba sai a ranar 25 ga watan Fabrerun bana. Ita ma tawagar masu bincike daga jami'ar London da sauran kwalejoji, sun nazarci sinadaran kwayoyin cutar daga mutane sama da 7,500 da suka kamu da ita a fadin duniya, kuma sun yi ammana cewa, an samu sabbin kwayoyin cutar ne daga karshen shekarar 2019. Ko a makaon da ya gabata ma wasu kwararru daga hukumar lafiya ta duniya WHO, sun iso kasar Sin don gudanar da bincike game da tushen cutar COVID-19, kuma mai yiwuwa ne aikin gano hakikanin tushen wannan cuta ba na gajeren lokaci ba ne, zai kuma iya shafar ziyartar kasashe da yankuna daban daban dake sassan duniya. Hakika ya kamata a dinga sara ana duba bakin gatari domin gudun kada a yi kitso da kwarkwata. (Marubuci: Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China