Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Me ya sa al'ummar Sinawa suke nuna cikakken goyon baya ga gwamnatin kasar Sin?
2020-07-19 15:43:33        cri
Kwanan baya, cibiyar Ash mai nazarin dimokuradiyya da aikin kirkire-kikire na kwalejin Kennedy ta jami'ar Harvard ta kasar Amurka ta gabatar da wani sakamakon bincike cewa, al'ummar Sinawa na kara nuna gamsuwa ga gwamnatin tsakiyar kasar tun bayan da cibiyar ta gudanar da wani bincike daga shekarar 2003. A ganin Sinawa, manufofin kasar da ayyukan da jami'an wurare daban-daban suka yi suna ta samun ingantuwa. Kuma kimanin kashi 90% na mutanen kasar suna gamsuwa da ayyukan da gwamnatin kasar Sin take yi.

To, me ya sa al'ummar Sinawa suke nuna cikakken goyon baya ga gwamnatin kasar Sin? Ban da wasu nagartattun manufofin da gwamnatin ta dauka a fannoni daban-daban, wadanda jama'a suke cin gajiya. Bari mu duba wasu hakikanin shaidu.

Na farko, bayan bullowar wannan mummunar cuta ta COVID-19 a kasar Sin, jama'a na cikin halin rashin tabbas, saboda sabuwar cuta ce da ba a taba ganinta a da ba. Gwamnatin kasar Sin ta dauki matakin killace birnin Wuhan don hana yaduwar cutar zuwa duk fadin kasar, tare kuma da tura masana mafi kwarewa zuwa birnin don fitar da dabaru mafi dacewa wajen yakar cutar. Ban da wannan kuma, gwamnatin na yanke shawarar yin iyakacin kokarin ceton rayukan mutane ba tare da yin la'akari da asarar kudade ba. Wato gwamnatin ta biya duk kudin da za a kashe wajen jiyyar wadanda suka kamu da cutar. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba nuna cewa, ya kamata a mayar da rayukan jama'a da bukatun jama'a a gaban kome. Shugaba Xi ya taba kai ziyarar birnin Wuhan don karawa jama'a da likitoci kwarin gwiwa yakar cutar. Saboda ganin yadda cutar take illata zaman rayuwar yau da kullum na jama'a, gwamnatin ta dauki wasu matakan tabbatar da farfado da tattalin arziki da ba da taimako ga al'umma wajen dawo bakin aiki.

Na biyu, an yi bala'in ambaliyar ruwa a wasu wuraren kasar Sin mai tsanani, shugaba Xi Jinping ya ba da umurnin ceton rayukan jama'a da yin iyakar kokarin bada tabbacin kariya ga dukiyoyin jama'a, da kuma bada kulawa yadda ya kamata ga wadanda bala'i ke ritsawa da su. Sojojin kasar na kokarin tinkarar wannan bala'i, duk da cewa akwai yiwuwar sadaukar da rayukansu, saboda dukkansu mambobin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ne, nauyin dake wuyan jam'iyyar JKS shi ne bautawa kasa da jama'a.

Na uku, wannan shekarar da muke ciki shekara mai muhimmanci ne wajen kawar da kangin talauci gaba daya a duk fadin kasar Sin. Tabbatar da zaman rayuwar jama'a cikin wadata wani muhimmin aiki ne dake gaban gwamnatin kasar Sin. Sin ba za ta bar ko wani wuri a baya ba, muhimmin muradu na hanyar tsarin mulki ta gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin shi ne taimakawa juna don samun wadata tare cikin al'umma.

To, ga wadannan shaidu, shin ko ka san dalilin da ya sa jama'ar kasar Sin suke nuna cikakken goyon baya ga gwamnatin kasar Sin da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin wadda ke jagorantar gwamnatin? (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China