Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan siyasar Amurka dake baza jita-jita kan batun Xinjiang suna keta hakkin bil Adama
2020-07-17 20:33:32        cri

Yan siyasar Amurka, kamar sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo, da mai ba da shawara kan harkokin tsaron kasar Robert O'Brien, na ci gaba da yada jita-jita kan manufar da kasar Sin take aiwatarwa a jihar Xinjiang, inda suka bayyana cewa, an tsare mutane da dama a jihar, kana an tilasta su yin aiki, har ma ana hana su haihuwa. Sun ce dukkanin irin wadannan matakai, keta hakkin bil Adama na al'ummar jihar ne, to sai dai kuma ba su nuna shaidu masu ma'ana ko kadan game da zargin da suke yayatawa ba.

Hakika, manufar gwamnatin kasar Sin a jihar Xinjiang ta kare hakkin bil Adama na al'ummun jihar ne. Alal misali, an dauki matakan yaki da ta'addanci da tsattsauren ra'ayi a jihar, kuma a sanadin haka, an dakile aukuwar harin ta'addanci a jihar a cikin shekaru 3 da suka gabata. A bayyane take cewa, ana tabbatar da hakkin kare rayukan al'ummun jihar yadda ya kamata. A sa'i daya kuma, gwamnatin jihar ta yi iyakacin kokari, domin samar da aikin yi gare su, kuma duk wadannan sun nuna cewa, ya dace al'ummun kasar Sin su yi sharhi kan yanayin kare hakkin bil Adama da kan su, kana bai kamata 'yan siyasar Amurka su tsoma baki a cikin harkokin gidan kasar Sin ba.

Amma kasar Amurka, a cikin shekaru kusan 20 da suka gabata, ta kai hari kasar Iraki, da kasar Libya, da sauran kasashe ba bisa ka'ida ba, kuma matakan aikin sojin da ta dauka sun jefa al'ummun kasashen da abin ya shafa cikin tsananin bukatar jin kai. Yanzu haka kuma, annobar cutar numfashi ta COVID-19 tana yaduwa cikin sauri a Amurka, kuma dalilin da ya sa hakan shi ne, gwamnatin kasar Amurka ba ta dauki matakan da suka dace a kan lokaci ba.

Kana yayin taron hukumar kare hakkin bil Adama ta MDD karo na 44 da aka kira kwanakin baya, kasashen duniya 46 sun fitar da wata hadaddiyar sanarwa, inda suka jinjinawa ci gaban da kasar Sin ta samu, wajen raya sha'anin kare hakkin bil Adama a jihar Xinjiang, tare kuma da sukar Amurka, bisa kashedin da ta yi wa kasar Sin game da batun hakkin bil Adama, lamarin da ya nuna cewa, yawancin kasashen duniya suna nacewa kan matsayin adalci.

Idan wadannan 'yan siyasar Amurka, suna son kara fahimtar yanayin da jihar Xinjiang ke ciki, ya dace su saurari ra'ayoyin da kasashen duniya suka cimma, kana ya fi kyau su ziyarci jihar don ganin abubuwan dake faruwa da idonsu kai tsaye. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China