Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wasu 'yan siyasar Amurka suna kawo babbar barazana ga zaman lafiyar duniya
2020-07-16 20:07:23        cri

A kwanakin baya bayan nan, kamar yadda sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo, da mai ba da shawara kan harkokin cinikayya na fadar White House Peter Navarro suka yi, shi ma mai ba da shawara kan harkokin tsaron kasar Amurka Robert O'Brien ya yada jita-jitar cewa, jam'iyyar kwaminis mai mulki a kasar Sin, tana kawo babbar barazana ga kasar Amurka da kasashe kawayan ta, kana ya zargi tsarin siyasa na kasar Sin kamar yadda yake so, amma hakika an gano cewa, makasudin sa na daukar wannan mataki shi ne, dora laifi kan wasu, tare kuma da kare moriyar siyasa ta su.

An lura cewa, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, wadannan 'yan siyasa sun dauki matakan da ba su dace ba da dama. Alal misali, tayar da rigingimun tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasarsu da kasar Sin, da danne kamfanonin kimiyya da fasahar zamani na kasar Sin, da yin ikirarin katse hulda da kasar Sin, da yin barazana ga hukumomin watsa labaran kasar Sin dake Amurka, da kawo illa ga cudanyar dake tsakanin al'ummun kasashen biyu, da zargin kasar Sin kamar yadda suke so, tun bayan barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19, har ma suna tsoma baki a cikin harkokin gida a yankin Hong Kong, da jihohin Xinjiang da Taiwan da Tibet, da kuma yankin kudancin teku na kasar Sin. To amma abun tambaya gare su shi ne, wane ne ke kawo barazana ga wani?

Hakika dalilin da ya sa 'yan siyasar Amurka suke daukan wadannan matakai shi ne, ba su son sauran kasashen duniya su samu ci gaba.

Ko shakka ba bu, kasar Sin ba za ta zamewa Amurka kalubale ba, kana ba za ta kasance wata Amurka ta daban ba, kuma makasudin ci gaban kasar Sin shi ne samar da wadata ga al'ummun kasar, tare kuma da farfado da al'ummun Sinawa, kana da tabbatar da zaman lafiya a fadin duniya.

Har kullum kasar Sin tana nacewa kan manufar daidaita sabanin dake tsakaninta da Amurka ta hanyar yin shawarwari, kana ba zai yiwu ta tsoma baki a cikin harkokin gidan sauran kasashe ba, amma tabbas ne za ta dauki mataki na wajibi domin kare hakki da moriyarta, shi ya sa yunkurin gyara kasar Sin na wasu 'yan siyasar Amurka ba zai yi nasara ba.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China