Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
GDP na kasar Sin ya karu da kaso 3.2 a rubu'i na biyu na bana
2020-07-16 11:27:26        cri
Hukumar kididdiga ta kasar Sin (NBS) ta sanar a yau Alhamis cewa, alkaluman GDPn kasar ya karu a rubu'i na biyu na shekarar bana, karuwar kaso 3.2 cikin 100 kan makamancin lokaci na bara.

A cewar alkaluman hukumar, a watanni 6 na farkon bana, GDPn kasar ya kai Yuan tiriliyan 45.66, kwatankwacin dala tiriliyan 6.53, raguwar kaso 1.6 cikin 100 kan na bara, hakan ya faru ne sakamakon tasirin COVID-19.

Jadawalin alkaluman ya nuna cewa, masana'antun dake samar da muhimman abubuwan sarrafa kayayyaki, sun samu karuwar kaso 0.9 kan na bara, yayin da sashen ba da hidima ya samu koma bayan kaso 1.6 sai bangaren masana'antun samar da kayayyaki ya samu koma baya na kaso 1.9 cikin 100 kan na bara.

Sai dai alkaluman da hukumar ta fitar a yau, sun nuna yadda kasuwar samar da ayyukan yi ta kasar Sin ta dan inganta a watan Yuni, inda rashin aikin yi a yankunan biranen kasar ya tsaya a kaso 5.7 cikin 100, wato kasa da kaso 0.2 cikin 100 kan na watan da ya gabata.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China