Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta inganta ayyukan kasuwanci, kirkire-kirkire da kara samar da ayyukan yi ga wasu muhimman sassa na alumma
2020-07-16 10:34:58        cri

Kasar Sin za ta bullo da wasu sabbin matakai don inganta harkokin kasuwanci da kirkire-kirkire, inda za a mayar da hankali musamman kan samar da ayyukan yi da kafa sabbin sana'o'i ga daliban da suka kammala kwalejoji da sauran muhimman sassa na al'umma.

An dai cimma wannan shawara ce, yayin zaman majalisar gudanarwar kasar na ranar Laraba wanda firaminista Li Keqiang ya jagoranta. Yana mai cewa, shirin inganta harkokin kasuwancin kasar gami da kirkire-kirkire, wani muhimman mataki ne, a fannin dorewa da fadada guraben ayyukan yi, da zakulo sabbin hanyoyin ci gaba.

Firaministan ya kuma bayyana bukatar dake akwai ta kara sanya harkokin kasuwanci da kirkire-kirkire da karfafa rawar da yake takawa wajen samar da ayyukan yi, musamman ga daliban da suka kammala kwalejoji.

Taron ya kuma bayyana muhimmancin kara zage damtse wajen samun daidaito kan sassa guda 6 da kuma tsaro a fannoni guda 6.

Bisa la'akari da kalubalen da cutar COVID-19 ta haddasa, da sauyin yanayi kan bunkasuwa, taron ya yi kira da a mayar da hankali kan yadda za a bunkasa kirkire-kirkire, da yadda ayyukan yi za su taimakawa al'umma da kuma kirkire-kirkire, don cin gajiyar karfin kasuwa da abubuwan da jama'a suka kirkiro.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China