Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin ya gayyaci jakadan Amurka dake Sin
2020-07-16 10:18:33        cri
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Zheng Zeguang, a jiya Laraba ya gayyaci jakadan Amurka dake kasar Sin Terry Branstad, don gabatar da rashin amincewar kasarsa kan dokar nan mai nasaba da 'yancin yankin Hong Kong da shugaban Amurka Donald Trump ya sanyawa hannu.

Zheng ya ce, dokar da kuma umarnin shugaban na Amurka, sun nuna rashin muhimmancin dokar tsaron kasa mai nasaba da yankin na Hong Kong, sun kuma cire duk wasu fifiko na musamman da ake baiwa yankin, har ma ya yi barazanar sanyawa kamfanoni na daidaikun Sinawa takunkumi. Wannan tamkar tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin, kuma hakan ya saba dokokin kasa da kasa da muhimmin ka'idojin alakar kasa da kasa. A don haka kasar Sin tana adawa da kakkausar murya kan wannan batu.

Ya ce, kasar Sin za ta dauki dukkan matakan da suka dace, don mayar da martani kan danyen aikin da Amurka ta aikata, domin ta kare muradunta, ciki har da sanyawa kamfanoni da wasu Amurkawa takunkumi.

Jami'in na kasar Sin ya ce, duba da cewa, Hong Kong, yankin musamman ne na kasar Sin, wannan ya sa kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar Sin ya tanada, zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin(NPC), da muhimman dokokin yankin da shawarwarin da majalisar ta NPC ta yanke, aka bullo da dokar tsaro a yankin na Hong Kong, kuma wannan batu ne da ya shafi harkokin cikin gidan kasar Sin, kuma babu wata kasar waje dake da ikon yin kalaman da ba su dace ba ko tsamo baki kan wannan batu. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China