Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ba zai yiwu Amurka ta yi wa Sin barazana ta hanyar kafa doka kan HK ba
2020-07-15 20:33:13        cri

A kwanakin baya bayan nan, gwamnatin kasar Amurka, ta sa hannu kan doka game da "mazauna Hong Kong su gudanar da harkokin yankin da kansu", wadda majalisar dokokin kasar ta zartas da ita, inda ta zargi dokar tsaron kasa ta yankin Hong Kong ta kasar Sin kamar yadda take so, har ta yi barazanar cewa, za ta kakaba wa kasar Sin takunkumi.

Matakin da Amurkan ta dauka tsoma baki ne a cikin harkokin gidan kasar Sin, haka kuma, ya saba wa dokokin kasa da kasa, da ka'idojin huldar kasa da kasa, lamarin da ya nuna cewa, wasu 'yan siyasar Amurka suna tayar da tarzoma a yankin Hong Kong, don haka matakin ya gamu da suka daga al'ummun kasa da kasa. Kuma ko shakka babu, yunkurin Amurka ba zai yi nasara ba.

Tun bayan da aka fara yin zanga-zanga a yankin Hong Kong a watan Yunin bara, wasu masu tayar da tarzoma, sun rika kai hari ga hukumomin jama'a na yankin a karkashin goyon bayan wasu kungiyoyin ketare, har ta kai ga sun lalata motoci, tare kuma da kai hari ga mazauna yankin. Duk wadannan sun kawo barazana mai tsanani ga tsaron kasar Sin. A daidai wannan lokaci, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin, ta zartas da dokar kare tsaron kasa ta yankin Hong Kong, wadda ke taka babbar rawa wajen kiyaye tsaro a yankin, kuma yawancin al'ummun kasa da kasa suna ganin cewa, kafa dokar ya dace da ka'idar doka, da bukatar yanayin yankin, da fatan jama'a, da kuma ka'idojin kasa da kasa, wadanda ke sa ran makomar yankin Hong Kong za ta kyautata suna goyon bayan dokar.

Amma wasu 'yan siyasa na Amurka, ba su so a tabbatar da kwanciyar hankali a Hong Kong, shi ya sa suke fitar da doka kan yankin, har ta kai suna yin barazana da cewa, za su kakaba wa kasar Sin takunkumi, matakan da suka dauka sun keta hakki da moriya na mazauna yankin Hong Kong, haka kuma sun nuna yunkurinsu na tayar da tarzoma a yankin.

Wadannan 'yan siyasa na Amurka sun sanar da cewa, za su kakabawa mutane, da hukumomin kudi, da sauran kamfanoni wadanda ke illata cin gashin kan Hong Kong takunkumi. To sai dai kuma matakin da suka dauka ya keta dokokin kasa da kasa, kuma hakan tsoma baki ne a cikin harkokin gidan kasar Sin.

Bisa sanarwar ka'idar dokokin kasa da kasa da aka zartas yayin babban taron MDD da aka kira a shekarar 1970, an bayyana cewa, kowace kasa, ko kowanen rukuni, ba shi da hurumin tsoma baki a cikin harkokin gida, ko harkokin diplomasiyya na sauran kasashe kai tsaye, ko ma ba ta kai tsaye ba.

Game da dokar da Amurkan ta sawa hannu, gwamnatin kasar Sin ta riga ta bayyana cewa, za ta mayar da martini na wajibi, wato za ta kakabawa jami'ai, da sassan da abin ya shafa na Amurka takunkumi, kuma ya dace 'yan siyasar Amurka su daina daukan matakan da ba su dace ba. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China