Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Farfadowar cinikin wajen Sin ya sa kaimi kan ci gaban aikin samar da kayayyaki a fadin duniya
2020-07-14 20:03:21        cri

A yau Talata ne babbar hukumar kwastam ta kasar Sin, ta fitar da sabbin alkaluman cinikin waje na kasar, inda ta bayyana cewa, a cikin watanni shida na farkon bana, adadin kudin da aka samu daga cinikin da ta yi da kasashen ketare ya kai kudin Sin yuan triliyan 14.24, duk da cewa, adadin ya ragu da kaso 3.2 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara.

Har wa yau alkaluman sun nuna cewa, adadin kudin da aka samu a rubu'in na biyu ya karu a bayyane, wato ya karu da kaso 3.3 bisa dari idan aka kwatanta da rubu'i na farko. Abun farin ciki shi ne, adadin kudin da aka samu daga fitar da kayayyaki zuwa ketare a watan Yunin da ya gabata, ya karu da kaso 4.3 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin bara.

Hakazaz lika adadin kudin da aka samu daga shigo da kayayyaki daga ketare kuwa, ya karu da kaso 6.2 bisa dari idan aka kwatanta da Yunin bara, lamarin da ya nuna cewa, a karon farko, fannin shige da fice na kasar Sin sun karu tare, wanda hakan ya shaida cewa, cinikin wajen kasar Sin yana farfadowa sannu a hankali.

Yanzu haka daukacin kasashen duniya suna fama da bazuwar annobar cutar numfashi ta COVID-19, amma cinikin wajen kasar Sin yana gudana yadda ya kamata, dalilin da ya sa haka shi ne, kasar Sin ta yi nasarar dakile yaduwar annobar a cikin gida, kana ta cimma burin komawa bakin aiki daga duk fannoni a fadin kasar. Ban da haka kasar Sin tana kara fitar da kayayyakin kiwon lafiya da al'ummun kasa da kasa suke bukata, domin kandagarkin annobar zuwa ketare. Alal misali, kayan rufe baki da hanci, da na'urorin likitanci, da magunguna da sauransu.

Bugu da kari, adadin na'urar kwanfuta da wayar salula da kasar Sin ta fitar zuwa kasashen waje shi ma ya karu, wato adadin kwanfuta ya karu da kaso 9.1 bisa dari, kana adadin wayar salula ya karu da kaso 0.2 bisa dari. A sa'i daya kuma, sayayya ta yanar gizo ta taimakawa harkokin cinikayya na kamfanonin cinikin wajen kasar Sin, yayin da suke fuskantar illolin da annobar COVID-19 ke haifarwa.

A daya wajen kuma, gwamnatin kasar Sin ta fara aiwatar da wasu manufofi tun farkon bana, domin ingiza ci gaban cinikin wajen kasar. Misali an shirya bikin baje kolin hajojin da ake shigowa da su kasar Sin, da wadanda ake fitarwa daga kasar da aka fi sani da "Canton Fair" ta yanar gizo.

An maido harkokin shige da fice, ta hanyar yin jigilar da kayayyaki ta jiragen kasa masu dakon kayayyaki tsakanin kasar Sin da kasashen Turai, kana an kara kafa wasu yankunan gwaji na kasuwanci ta yanar gizo tsakanin kasa da kasa.

Duk wadannan sun nuna cewa, cinikin waje na kasar Sin yana samun ci gaba lami lafiya, yana kuma taka rawar gani a fannin karuwar tattalin arzikin duniya, da kuma kara habaka cudanyar tattalin arzikin duniya baki daya. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China