Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ta Yaya Za Mu Iya Ganin Bayan Cutar COVID-19?
2020-07-11 17:28:48        cri

Cutar COVID-19 na ci gaba da yaduwa a duniya, inda a ranar Alhamis da ta gabata kadai, aka samu karin wasu 204938 da suka kamu da cutar a kasashe daban daban. Sai dai ko muna da damar shawo kan wannan cuta? Kuma ta yaya za mu iya cin nasarar dakile ta? Don amsa wadannan tambayoyi, za mu iya duba misalin wasu matakan da aka dauka a birnin Beijing na kasar Sin a kwanakin baya.

Tun daga ranar 11 ga watan Yunin da ya gabata, a wata babbar kasuwar birnin Beijing, an gano wasu mutane masu dauke da kwayoyin cutar COVID-19. Daga bisani hukumomin birnin sun dauki jerin matakai cikin sauri, wadanda suka hada da rufe kasuwar, da ungwannin dake kewayen ta, da binciken abubuwan dake cikin kasuwar don gano asalin cutar, da gudanar da gwajin kwayoyin cuta kan dimbin mutane, don samun mutanen da suka kamu da cutar cikin sauri, kafin cutar ta kara yaduwa.

Cikin wadannan matakai, wanda ya fi burge ni shi ne gudanar da gwaji kan tarin mutane. Zuwa ranar 6 ga watan Yulin da muke ciki, wato kusan wata daya bayan samun barkewar cutar a Beijing, an gudanar da gwaji kan mutane fiye da miliyan 11 a birnin. Inda aka samu wasu 335 da suka kamu da cutar COVID-19, sa'an nan aka kwantar da su cikin asibiti. Zuwa lokacin da na rubuta wannan bayani, wasu 72 daga cikinsu sun riga sun warke, wadanda aka sallame su daga asibiti. Sa'an nan ba wanda ya mutu a cikin dukkan masu dauke da cutar.

Dalilin da ya sa batun nan na gwaji ya burge ni sosai, shi ne na taba raka wasu abokaina zuwa wurin gwajin. Saboda wadannan abokai nawa sun taba zuwa wata kasuwa, inda aka samu wani mai dauke da cutar COVID-19, don haka wasu alkaluman da hukumomin suka samu ta hanyar wayar salular daidaikun mutane, sun nuna cewa abokaina sun taba zuwa wurin da ake samun cuta, ta yadda suka fuskanci hadarin kamuwa da cuta.

Daga baya, jami'ai masu kula da unguwa sun tuntubi abokaina, domin su je wani wurin bincike, inda za a yi musu gwaji. Daga baya, abokaina sun tafi wani wurin binciken da aka kafa cikin wani babban filin wasa, inda mutane suka shiga layi don jiran a yi musu bincike, karkashin jagorancin jami'ai na ungwanni. Sa'an nan ba tare da wani jinkiri, ko kuma bata lokaci ba, mutum dake gaban layin sai ya zauna, wani likita ya sanya wani abu cikin bakinsa, ya dan goga don samun miyau dake cikin makogwaro.

Cikin dakikoki 2 za a gama wannan aiki, sa'an nan mutum zai iya komawa gida. Cikin sa'o'i 48, idan ba a sanar masa cewa ya kamu da cutar ba, to, hakan na nufin ba ya dauke da kwayar cutar COVID-19. Idan hukumomi sun sa ka je a yi maka bincike ne, bisa tuhumar yiwuwarka ta kamuwa da cuta, to, ba ka bukatar biyan ko kwabo daya. Sa'an nan idan ka nemi a yi maka gwaji bisa son ranka, don neman kau da damuwa, to, za a karbi kudi, amma kadan ne. Ta wannan hanya ana neman sanya mafi yawan al'umma samun gwajin kwayoyin cuta, ta yadda za a iya gano wadanda suka kamu da cutar cikin sauri.

Ana gudanar da wadannan matakai ne tamkar matakin da a kan dauka don kashe gobara. Kun san idan gobara ta tashi, to ya zama dole a kashe ta cikin sauri. In ba haka ba, idan gobarar ta yadu zuwa wurare daban daban, to, ba yadda za a yi, sai dai barin ginin ya kone kurmus. Don haka, hukumar Beijing ta yi iyakacin kokarinta don gano masu dauke da cutar, da killace su, gami da kula da su, ta yadda cutar ba za ta kara yaduwa tsakanin al'umma ba.

To amma shin ko wannan niyyar ta yi amfani? Zuwa lokacin da na rubuta wannan bayani, ba a sake samun sabon wani mutum da ya kamu da cutar COVID-19 ba cikin jerin wasu kwanaki. Hakan na nufin cewa kwalliya ta biya kudin sabulu.

Amma nasarar da birnin Beijing ta samu a fannin dakile yaduwar cuta, ta nuna cewa, za a iya ganin bayan cutar a birnin Beijing da kuma kasar Sin ke nan? Ba haka ba ne. Domin har yanzu ana ta samun sabbin masu dauke da cutar da suke shigawa kasar Sin daga ketare. Misali a ranar jumma'a, an gano wasu mutum 4 da suka shigo kasar dauke da cutar COVID-19. Don haka irin wadannan matakai da ake aiwatarwa suna da amfani, sai dai dole ne a kawar da cutar a duniyarmu gaba daya, sannan ne kawai za a samu ganin bayan cutar baki daya, amma kafin hakan, annobar za ta iya dinga dawowa a kai a kai.

Sai dai ta yaya za mu iya kawar da cutar baki daya daga doron kasa? Za a bukaci hadin gwiwar kasashe daban daban, inda za su dinga musayar fasahohi, da magunguna, da kwararru, da kayayyaki, da kudi, don taimakawa juna tinkarar annobar, ba tare da barin wata kasa a baya ba.

Ta wannan hanya kadai, ana iya samun damar kashe gobarar annoba kacokan, ba tare da sake samun tasowarta ba.

Abin takaici shi ne, har yanzu ana ta samun rarrabuwar kai tsakanin kasashe daban daban. Misali, kasar Amurka ta sanar da janyewarta daga hukumar lafiya ta duniya WHO a kwanan baya. Sa'an nan wasu 'yan siyasa suna ta kokarin dora laifi ga sauran kasashe, maimakon dora cikakken muhimmanci kan aikin yakar annoba. Maimakon su amince da matakin gudu tare a tsira tare, suna neman jefa sauran kasashe cikin matsaloli, ta yadda suke cin tura a gida ba zai zama mai muni sosai ba.

Ko shakka babu, idan sun ci gaba da yin haka, ba za mu san yaushe za a samu damar ganin bayan cutar COVID-19 a duniyarmu ba. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China