Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
China CPC: Hankalin duniya ya karkata kan cika shekaru 99 da kafuwar JKS
2020-07-06 16:43:00        cri

 

Masu hikimar magana na cewa tafiya sannu-sannu kwana nesa, a wannan shekarar ne ake cika shekaru 99 da kafuwar jam'iyya mafi girma a duniya wacce ke da dunbun magoya baya wato jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ko kuma JKS a takaice. A bisa kiyasi jam'iyyar tana da magoya baya da yawansu ya doshi miliyan 90. A matsayinta na jam'iyya mai mulki mafi girma a duniya, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin tana nuna himma da kwazo wajen kare muradun jama'ar kasar, wadda ke samun amincewa da cikakken goyon-baya daga wajensu. A yayin da kasar Sin ke kokarin ganin bayan annobar COVID-19 a wannan karo, ko tsoffi, ko jarirai, ko mawadata, ko matalauta, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ba ta bar kowa a baya ba, hatta ma tana iyakacin kokarinta wajen ceto wadanda suka kamu da cutar, al'amarin da ya sake shaida cewa, jam'iyyar tana maida rayuwar al'umma a gaban kome. Lallai idan mun lura, za mu iya cewa tasirin da JKS ke da shi bai kebanta kan kasar Sin kawai ba, domin kuwa tasirin jam'iyyar ya game dukkan kasa da kasa, alal misali, a wannan lokaci da ake cika shekaru 99 da kafuwarta, sama da jam'iyyun siyasa 100 na kasashen duniya ne suka taya babban sakataren kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin CPC Xi Jinping, murnar cika shekaru 99 da kafuwar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin wanda ya fado a farkon watan Yuli, jam'iyyun siyasun duniya sun yaba da irin dinbin tarihin da jam'iyyar JKS ta kafa, da kuma manyan nasarorin da kasar Sin ta cimma. A sakon da suka aika zuwa ga sashen hulda da kasa da kasa na kwamitin tsakiyar CPC, jami'iyyun siyasar sun ce, sun yi amanna cewa kasar Sin karkashin jagorancin jam'iyyar CPC, babu tantama za ta kai ga matsayi mai haske a nan gaba kana za ta bayar da babbar gudunmawa ga ci gaban dukkan bil adama. Jam'iyyun siyasa da dama na duniya sun bayyana ra'ayoyinsu game da cika shekaru 99 da kafuwar CPC, misali, jam'iyyar kwaminis ta kasar Masar ECP, tana da ra'ayin cewa a shekaru 99 da suka gabata, jam'iyyar CPC ta jagoranci al'ummar Sinawa wajen cimma muhimman nasarori ta fuskar bunkasuwar al'amurran siyasa, tattalin arziki, zaman rayuwar al'umma, da sauran fannoni, kana ta bayar da gagarumar gudunmawa ga yunkurin da duniya ke yi na yakar mulkin danniya, da mulkin mallaka, da kuma tabbatar da adalci a duniya baki daya. Ita ma jam'iyyar ANC mai mulkin Afrika ta kudu ta ce, kafuwar jam'iyyar CPC yana da matukar muhimmanci ga tarihin Sinawa da ma daukacin mutanen duniya. A nata bangaren jam'iyyar Nasdem ta kasar Indonesia ta yi tsokaci cewa karkashin jagorancin JKS kasar Sin ta yi nasarar dakile manyan kalubalen dake shafar annobar COVID-19, kuma ta cimma manyan nasarori wajen bunkasa tattalin arzikin kasar. Ko shakka babu, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta taka rawar gani ga ci gaban al'amurran siyasa, tattalin arziki da zamantakewar kasa da kasa, da ma 'yan magana kan ce mai kamar zuwa ake aika. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China