Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gaskiya da karya ba za su taba haduwa ba
2020-07-05 22:04:09        cri

 

 

Yanzu haka, hukumar kare hakkin dan-Adam ta MDD tana gudanar da zamanta a karo na 44 a birnin Geneva. A taron da aka gudanar a ranar Larabar da ta gabata, a madadin kasashe 46, kasar Belarus ta gabatar da jawabi, inda suka bayyana goyon bayansu kan matakan yaki da ta'addanci da kawar da tsattsuran ra'ayi da Sin take dauka a yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa.

A jawabin da ta gabatar, Belarus ta ce, ta'addanci da tsattsauran ra'ayi abokan gaba na bai daya ne ga dukkanin 'yan Adam, haka kuma mummunar barazana ce ga hakkin bil Adam. Tana mai cewa, mun lura da barnar da al'ummar yankin Xinjiang 'yan kabilu daban daban suka sha sakamakon ta'addanci da ra'ayin jawo baraka ga kasa da kuma tsattsauran ra'ayi, kuma mun yaba jerin matakan da kasar Sin ta dauka na shawo kan barazanar da kare hakkin bil Adam na al'ummar yankin. A cikin shekaru uku a jere, ba a kai harin ta'addaci ko sau daya a jihar ba. Abin da ke alamta cewa, an dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar ta Xinjiang.

Baya ga haka, a zaman taron da ya gudana a ranar 30 ga watan Yunin da ya gabata, a madadin kasashe 53, kasar Cuba ta yi maraba da yadda majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta zartas da dokar kare tsaron kasa mai nasaba da yankin musamman na Hong Kong na kasar, kafin daga bisani wakilan wasu kasashe sama da 20 suka bayyana goyon bayansu ga dokar a ranar 1 da kuma ranar 2 ga watan nan da muke ciki.

A jawabin da wakilin kasar Rasha ya gabatar, ya ce Rasha na nuna tsayayyen goyon baya ga kasar Sin wajen aiwatar da manufar"kasa daya amma tsarin mulki iri biyu" a yankin musamman na Hong Kong, kuma al'amurran Hong Kong batu ne na cikin gidan kasar Sin.

Sai kuma kasar Burundi a nata bangare ta yi maraba da kokarin da kasar Sin ta yi da kuma gudummawar da ta bayar ta fannin kare hakkin bil Adam, ta kuma nuna jinjinawa kan yadda majalisar wakilan jama'ar kasar ta zartas da dokar kare tsaron kasa mai nasaba da yankin musamman na Hong Kong. A cewarta, hakan zai tabbatar da kare hakkin bil Adam ga mazauna yankin Hong Kong. Ta ce, Hong Kong da kuma Xinjiang wasu sassa ne na kasar Sin da ba za a iya raba su ba daga kasar, kuma ta bukaci kasashen da abin ya shafa da su daina tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasar Sin bisa dalili na wai hakkin bil Adam.

Baya ga haka, wakilan kasashen Nijeriya da Indonesia da Vietnam da Bahrain da Sudan da Aljeriya da Morroco ma sun bayyana cewa, ya kamata kasa da kasa su bi ka'idar kaucewa tsoma baki cikin harkokin gida na sauran kasashe, sun kuma nuna kyamar yin shisshigi cikin harkokin cikin gida na wasu kasashe bisa hujjar kare hakkin bil Adam.

Lalle, kamar yadda malam bahaushe kan ce, gaskiya da karya ba za su taba haduwa ba. Yadda kasashen suka nuna goyon bayansu ga kasar Sin ya shaida kokarin da daukacin al'ummar duniya ke yi na kare adalci da gaskiya.

A hakika, batun Xinjiang ba ya shafar hakkin bil Adam ko kabila ko kuma addini, sai dai batu ne da ya shafi aikin yaki da ta'addanci da kuma jawo baraka ga kasa. A wannan fanni kuma, kasar Sin ta dauki kwararan matakai tare da cimma gagaruman nasarori, kuma an tabbatar da hakkin bil Adam na al'ummar yankin 'yan kabilu daban daban cikin kwanciyar hankali, lamarin da kuma ya samu amincewa daga kasa da kasa.

Domin cimma manufarsu ta siyasa ce ya sa wasu kasashe suka yi ta shafa wa kasar Sin bakin fenti a kan batun Hong Kong da na Xinjiang, inda suka gurbata gaskiya tare da tsoma baki a harkokin cikin gida na kasar Sin. Sai dai wadannan kasashe su kansu suna fuskantar munanan matsaloli na hakkin bil Adam, ciki har da matsalar kabilanci da korar baki da cin zarafin al'umma da 'yan sanda ke yi da sauransu. To, shin yaushe ne za su mai da hankali kan warware matsalolinsu na kansu a maimakon nuna fuska biyu? (Lubabatu Lei)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China