Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wani kamfanin kasar Sin yana taimakawa kasar Namibia farfado da tattalin arziki
2020-07-04 16:36:58        cri
Wani aikin hakar ma'adini na Uranium a wani wurin dake kasar Namibia, ya kasance daya daga cikin manyan ayyukan da ake gudanar da su, bisa hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka, gami da shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" da kasar Sin ta gabatar. Wani kamfanin kasar Sin mai suna CGN Swakop Uranium, yana kula da aikin na hakar Uranium, inda shugaban kamfanin Cai Yusheng ya ce, kudin da kamfaninsa ke samu a duk shekara ya kai kashi 5% na jimillar GDP, wato yawan kudin kayayyakin da ake samarwa a cikin kasar Namibia. Kana kayayyakin da kamfanin ke shiga da fitarwa, sun kai kashi 30% zuwa kashi 40% na dukkan kayayyakin da ake shiga da fitar da su ta tashar jirgin ruwa ta Walvis Bay, yayin da darajar kayayyakin ta kai kashi 20% na darajar daukacin kayayyakin da ake shiga da fitar da su a kasar ta Namibia. Saboda haka, a cewar shugaban kamfanin, yadda kamfaninsa ya maido da aikinsa zai sa kaimi ga farfadowar tattalin arzikin kasar daga mummunar illar da cutar COVID-19 ta haifar.

Bayan fara samun masu kamuwa da cutar a kasar Namibia, kamfanin CGN Swakop Uranium na kasar Sin, ya yi kokarin taimakawa al'ummar kasar, inda darajar kayayyakin kandagarkin cuta da kamfanin ya ba asibitoci, da makarantu, da ofisoshin 'yan sanda kyauta, ya kusan kai wa Naira miliyan 165, lamarin da ya karfafawa al'ummun kasar gwiwarsu a kokarinsu na dakile yaduwar cutar COVID-19. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China