Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Botswana ta karyata rahotannin mutuwar giwaye 356 cikin wata uku
2020-07-03 11:19:43        cri

A ranar Alhamis kasar Botswana ta karyata rahotannin da wasu kafafen yada labaran yammacin duniya suka yada dake bayyana mutuwar giwaye kimanin 356 a sanannen yankin kasar na Okavango Delta, dake arewa maso yammacin kasar ta kudancin Afrika.

Kenneth Maselesele, mai rikon mukamin babban sakataren ma'aikatar kare muhalli da kiyaye albarkatun kasa da yawon bude ido na kasar Botswana, ya amince cewa, giwayen suna mutuwa, amma adadin bai kai yadda wasu kasashen yamma suke zuzutawa ba.

Maselesele ya ce, biyo bayan gagarumar mutuwar giwayen da aka samu a yankunan Seronga dake arewa maso yammacin kasar Botswana, tun daga watan Maris na shekarar 2020 zuwa yanzu, giwaye 275 ne aka tabbatar sun mutu, sabanin 356 da ake yadawa.

A cewar Maselesele, wasu dakunan gwaje gwaje uku a kasar Zimbabwe, da Afrika ta kudu da Canada, suna kokarin tantance samfurorin da aka tattaro na gawarwakin giwayen, kuma za'a gudanar da bincike kan musabbabin mutuwar giwayen.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China