Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Karya Ta kare Kwarnafi ya kar Tsami
2020-07-01 16:26:10        cri
Masu iya magana na cewa, karya ta kare, wai Bori ya kar Boka, yanzu dai an kawo karshen duk wani guna-guni da gutsiri tsoma game da dokar tsaron yankin musamman na Hong Kong, bayan da zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar Sin ya jefa kuri'ar amincewa da dokar tsaron kasa da aka samar, domin tabbatar da tsaro a yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin.

Dokar ta samu amincewar majalisar ce, yayin zama na 20 na zaunannen kwamitin kolin JKS ta 13 ya da gudana ranar Laraba 30 ga watan Yunin shekarar 2020.

Kaza lika zaunannen kwamitin kolin ya amince da sanya dokar ciki sashe na III na Babbar Dokar da ake amfani da ita a yau da kullum a yankin na Hong Kong.

Sai dai a yayin da wasu kasashe da ma wadanda suka san ya kamata ke maraba da kafa wannan doka a yankin musamman na Hong Kong, a hannu guda kuma wasu 'yan siyasar Amurka da 'yan barandansu dake neman fakewa da Guzuma domin su harbi Karsana, ke adawa da dokar. Bakin Alkalami dai ya riga ya bushe. A ganinsu, idan har gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta kara inganta dokar kiyaye tsaron kasa ta yankin Hong Kong, ba za su samu damar yin shisshigi a harkokin yankin ba, sannan yunkurinsu na kawo tsaiko ga ci gaban kasar Sin ta hanyar fakewa da yankin na Hong Kong ba zai yi nasara ba. Ai da ma sai Bango ya tsage Kadangare ke samun wurin Shiga.

Sanin kowa ne cewa, kiyaye tsaron kasa, batu ne da ya shafi muhimman muradun kowace kasa a duniya. Kuma tun bayan da yankin Hong Kong ya dawo hannun kasar Sin, bisa ka'ida ta 23 cikin Babbar Dokar Hong Kong, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta dankawa yankin izinin kafa dokarta ta fannin kiyaye tsaron kasa. Amma kawo yanzu, ba'a kammala aikin kafa dokar ba, al'amarin da ya sa Hong Kong ya zama wani wurin dake fuskantar rashin doka a bangaren tsaron kasa.

Duk mai bibiyar al'amuran yau da kullum, ya ga yadda a shekarar 2019 da ta gabata, wasu bata-gari suka yi yunkurin balle Hong Kong daga kasar Sin, da cin zarafi gami da lalata tambari da tutar kasa, da zuga al'umma don su mamaye ofishin gwamnatin tsakiya dake Hong Kong, da kai hari kan mai uwa da wabi, da cin zarafin 'yan sanda wadanda a kullum suke sadaukar da rayukansu don tabbatar da tsaron al'umma, al'amuran da suka kasance ayyukan ta'addanci, da haifar da babbar barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a Hong Kong gami da cikakken iko na kasa. Kuma duk wata kasa da ta san abin da take yi, ba za ta amince da irin wannan danyen aiki ba.

Kamar kowace kasa mai cikakken 'yanci, ita ma kasar Sin tana da 'yancin kafa dokokin da za su dace da yanayi da ma tsarin tafiyar da cikakkun yankunanta. Kuma kafawa, da fara aiwatar da dokar tsaron kasa mai nasaba da yankin Hong Kong, wata muhimmiyar dama ce ta yanke hukunci ga baragurbin dake neman ta da rikici a yankin, lamarin da zai tabbatar da ci gaba mai dorewa a yankin, da ma tafiyar da tsarin nan na kasa daya amma tsarin mulki iri biyu. Haka kuma jagororin yankin sun sha nanata cewa, masu bin doka za su yi maraba da dokar tsaron da aka kafa, matakin da zai kara janyo masu sha'awar zuba da neman halaliya tare da kara dawo da martabar yankin a idon duniya.

Abin tambaya shi ne, wai rashin doka ne ya haifar da boren dake faruwa a sassan Amurka ko mene ne? Idan haka ne, abin da Amurkar ke fatan ganin yana faruwa ke nan a wasu kasashe? Idan bore shi ne adon 'yanci a bangaren Amurka, to hakika ba haka lamarin yake a sauran kasashe na duniya ba, burin kasashe masu 'yanci dake kishin muhimman muradun al'ummominsu, shi ne kare rayuka da dukiyoyin jama'a maimakon zangar-zangar da za ta kai ga koman bayan kasa da al'ummarta a dukkan fannoni. Da ma an ce, kowa da irin kiwon da ya karbe shi, wai makwabcin mai Akuya ya sayi Kura.

Duk wata kasa mai cikakken 'yanci, wajibi ne tana da dokar tsaron kasarta. Kuma duk wanda ya karya doka, ya kwana da sanin cewa, doka za ta taka shi. "Icce aka ce, tun yana danye ake lankwasa shi". (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China