Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin a Nijer ya halarci bikin mika tallafin kayan abinci da gwamnatin Sin ta samar
2020-07-01 13:37:31        cri

A ranar 30 ga watan Yuni, an gudanar da bikin mika tallafin kayan abinci wanda gwamnatin Sin ta samar ga Jamhuriyar Nijer, a Niamey, babban birnin kasar.

Jakadan Sin da ke Nijer Zhang Lijun ya ce, ambaliyar ruwa da bala'in farin da aka samu a wannan shekarar ya jefa mutane miliyan biyu cikin fargabar bala'in yunwa a Nijer, yayin da annobar COVID-19 da ta barke ba zato ba tsammani ita ma ta shafi zaman rayuwar jama'a miliyan 1.2 a kasar, lamarin da ya haifar da manyan kalubalolin karancin abinci. Shirin samar da tallafin abinci na gwamnatin Sin zai amfanawa mutane daga shiyyoyi 8 na Jamhuriyar Nijer. Kasar Sin za ta ci gaba da dora muhimmanci kan hadin gwiwar bangarorin biyu a fannonin kiwon lafiya da samar da abinci, tare da fatan al'ummomin kasashen biyu za su ci moriyar kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Nijer.

A madadin shugaban kasar, da gwamnatin kasar da ma al'ummar kasar ta Nijer, ministan hukumar ayyukan jin kan bil adama na jamhuriyar Nijer, Magaji Laouan, ya yabawa kasar Sin sakamakon samar da tallafin abincin ga kasar Nijer, ya ce a matsayinta na daya daga cikin muhimman abokan hadin gwiwar Nijer, kasar Sin tana bayar da taimako ga Nijer a lokutan da kasar ta fi tsananin bukatarsa, wanda a cewar ministan hakan ya kara bayyana kyakkyawar abota da alakar gaskiya tsakanin kasashen biyu. An yi amanna cewa bisa hadin gwiwar bangarorin biyu, dangantakar dake tsakanin kasashen zata kai zuwa wani sabon matsayi a nan gaba.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China