Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kenya ta samu karin kashi 14% na fitar da haja ketare a rubu'in farko na bana
2020-07-01 11:11:38        cri

Hukumar kididdigar kasar Kenya KNBS, ta sanar cewa kasar ta samu karin kashi 14 bisa 100 na kayayyakin da take fitarwa zuwa kasashen ketare daga kudin kasar shillings biliyan 157.7 kwatankwacin dala biliyan 1.48 a rubu'in farko na shekarar 2019 zuwa dala biliyan 1.68 a rubu'in farko na shekarar 2020.

Hukumar KNBS ta ce, jimillar kayayyakin da kasar Kenya ta fitar zuwa nahiyar Asiya ta karu daga dala miliyan 383 a rubu'in farko na shekarar 2019 zuwa dala miliyan 411 a makamancin lokacin na bana.

KNBS ta ce an samu karuwar hajojin da Kenya ta fitar zuwa hadaddiyar daular Larabawa da kashi 24.0% da kuma kasar Sin da kashi 23.9%.

A cewar hukumar kididdigar, babban abin da ya taimakawa kasar a bangaren fitar da kayayyakinta zuwa ketare sun hada da fannin fitar da ganyen shayi zuwa hadaddiyar daular Larabawa, da ma'adanin dutse mai daraja, da wasu sinadaren hada lemuka da take fitarwa zuwa kasar Sin, da kuma kara adadin man kananzir da take fitarwa zuwa wadannan kasashen biyu.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China