Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Iran za ta gurfanar da shugaban Amurka da wasu jamian kasar bisa laifin kisan Soleimani
2020-06-30 10:46:22        cri

Iran ta nemi hukumar 'yan sandan kasa da kasa Interpol, ta kama wasu jami'an siyasa da na sojin Amurka, wadanda ke da hannu a kisan janar Qassem Soleimani a watan Junairu.

Babban mai gabatar da kara na kasar Iran, janar Ali Qasi Mehr, ya ce an gabatar da sunayen jami'an Amurka 36, ciki har da shugaban kasar Donald Trump, ga hukumar Interpol.

Ya ce ana zargin mutanen da kisan kai da ayyukan ta'addanci, kan babban kwamandan na Iran.

Wani hari ta sama da Amurka ta kai ranar 3 ga watan Janairu ne ya yi sanadin mutuwar Qassem Soleimani, tsohon kwamandan rundunar juyin juya hali na kasar Iran, tare da wani kwamanda, a kusa da filin jirgin saman Baghdad. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China