Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Pompeo yana neman bata huldar dake tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin
2020-06-29 20:10:32        cri

Mike Pompeo, sakataren harkokin wajen kasar Amurka, ya sake bayyana wasu maganganu marasa hankali a kwanan baya, inda ya ce wai kasar Sin ba za ta cika alkawarin da ta dauka na tallafawa kasashen Afirka ba, da neman shafa bakin fenti ga taron kolin musamman na hadin gwiwar kasashen Afirka da kasar Sin, a kokarin dakile yaduwar cutar COVID-19.

Abin takaici shi ne, a lokacin da ake samun masu kamu da cutar COVID-19 masu tarin yawa a kasar Amurka, da sauran kasashen daban daban, mista Pompeo ba ya son mai da hankalinsa kan aikin yakar annoba. Maimakon haka, yana ci gaba da kokarin ta da zaune tsaye a duniya, da neman lalata huldar hadin kai da ake samu tsakanin kasashe daban daban a fannin tinkarar annobar.

Hakika wace ce aminiyar gaske ta nahiyar Afirka? Kana wace kasa ce ke yin alkawarin tallafawa nahiyar Afirka amma ba tare da cika shi ba? Dangane da wadannan tambayoyi, jama'ar kasashen Afirka sun san amsa sosai. Don haka yunkurin mista Pompeo na bata huldar dake tsakanin Sin da Afirka sam ba zai yi amfani ba. Kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewar, kasar Sin ce kawa da aminiya ta kasashen Afirka. Bayan abkuwar annobar COVID-19 a duniya, bangarorin Sin da Afirka sun yi kokarin taimakawa juna. Inda kasar Sin ta kula da 'yan Afirka dake kasar kamar yadda take kula da Sinawa, lamarin da ya sanya dalibai 'yan kasashen Afirka fiye da dubu 3 da suke karatu a lardin Hubei da birnin Wuhan na kasar Sin sun samu kulawa sosai. Ban da daya daga cikinsu da ya kamu da cutar COVID-19, tare da samun kulawa da warkewa cikin sauri, sauransu suna cikin koshin lafiya, ba su taba kamuwa da cutar ba.

Ban da wannan kuma, kullum kasar Sin tana kokarin cika alkawarin da ta yi yayin da take samar da tallafi ga nahiyar Afirka.

Bayan bullar cutar a nahiyar Afirka, kasar Sin ta kai dauki ga nahiyar cikin gaggawa, inda ta samar da dimbin kayayyakin kandagarkin cuta ga kasashen Afirka da kungiyar tarayyar Afirka AU, gami da tura tawagogin masana masu ilimin aikin jinya zuwa wasu kasashe 11, da kira tarukan musayar ra'ayi tsakanin kwararru da jami'ai masu kula da aikin dakile cutar COVID-19 fiye da 30 tsakanin bangarorin Sin da Afirka, da shirya kwas na horaswa kusan 400, tare da sanya tawagogin likitocin kasar Sin wasu 46, wadanda suke gudanar da aikin agaji a fannin likitanci a kasashen Afirka, su ma sun shiga aikin hana yaduwar cutar COVID-19 a kasashen da suke ciki.

Haka zalika, a wajen taron koli game da hadin gwiwar Sin da Afirka a kokarin dakile cutar COVID-19 da ya gudana a kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada bukatar kafa wani cikakken tsari na hadin gwiwa tsakanin bangarorin Sin da Afirka, a kokarin kare lafiyar jama'ar bangarorin 2, gami da alkawarin fara raba wa kasashen Afirka allurar rigakafin cutar COVID-19, bayan da kasar Sin ta kammala aikin nazarin allurar, da yafe wa wasu kasashen dake nahiyar Afirka bashin da kasar Sin ke binsu, wanda da ma ya kamata su mayar da kudin kafin karshen shekarar 2020 da muke ciki.

Shugaban kwamitin kungiyar tarayyar Afirka AU, Moussa Faki Mahamat, ya ce ba wani abun zai iya canza ko kuma bata huldar abota dake tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin. Wannan magana ta nuna ra'ayin jama'ar kasashen Afirka dangane da huldar dake tsakanin Afirka da Sin. Don haka zai fi dacewa, mista Pompeo ya daina mummunan aikin da yake yi, don ya mai da hankali kan batun hana yaduwar cutar COVID-19 a kasarsa ta Amurka. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China