Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin COMAC na kasar Sin ya mika jiragen sama 3 samfurin ARJ21 ga wasu manyan kamfanonin jiragen kasar
2020-06-29 11:07:22        cri

An mika jiragen saman fasinja 3 samfurin ARJ21, ga manyan kamfanonin jiragen saman kasar Sin, jiya Lahadi a Shanghai, matakin da ya sanya jirgin kirar kasar Sin shiga kasuwar sufurin jiragen sama ta cikin gida.

Kamfanin kera jiragen sama na kasar Sin COMAC ne ya mika jiragen masu kujeru 90 na sashen rahusa, ga kamfanonin jiragen saman Air China da China Eastern Airlines da kuma China Southern Airlines a cibiyarsa ta Pudong dake harhada jirage.

Daraktan sashen talla da ciniki na kamfanin COMAC, Zhang Xiaoguang, ya ce mika jiragen samfurin ARJ21 ga manyan kamfanonin 3, na nufin samfurin jirgin zai shiga kasuwar sufurin jiragen sama ta kasar Sin. Ya ce za a samu ingantuwar dabarun wayar da kan fasinjoji da tsarin tafiyarsa da na tallarsa.

Zuwa yanzu kamfanin COMAC ya samar da jimillar jiragen ARJ21 guda 32. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China