Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan masu yawon bude ido da Sin ta karba a cikin gida a bikin Duanwu ya kai fiye da miliyan 48
2020-06-28 17:10:14        cri
Hukumar raya al'adu da yawon shakatawa ta kasar Sin ta bada kididdiga cewa, yayin bikin Duanwu na kwanaki 3, yawan masu yawon bude ido da Sin ta karba a cikin gida ya kai fiye da miliyan 48, wato ya kai kashi 50.9 cikin dari bisa na shekarar bara. Sannan yawan kudin shigar da aka samu a wannan fanni ya kai biliyan 12.28, wato ya farfaro ya kai kashi 31.2% bisa na shekarar bara. Ban da wanna kuma, yawon shakatawa ta hanyar tuka motoci, da yawon bude ido a kewayen birane da bude ido a wuraren dake da alaka da al'adu sun zama babban karfin farfado da kasuwar yawon bude ido.

Kayayyakin tarihi na al' adu na samun karbuwa matuka daga masu bude ido, yawancinsu na son shiga ayyukan da aka gudanar a irin wadannan wurare, don more rayuwar wurin. An ce, hada al'adun gargajiya da salon gargajiya na kasar Sin tare, ya zama sabon matakin jawo hankali masu sayayya, kashi 92.4% na masu yawon bude ido sun shiga ayyukan al'adu, daga cikinsu kashi 44.7% sun kai ziyara a titunan gargajiya.

Muhimmin hali a yayin bikin Duwanwu ta fuskar yawon bude ido shi ne "Yin kandagarkin cutar COVID 19 tare da yawon bude ido", alal misali, yin rajista ta kafar Intanet da rarraba abinci da kusantar da juna har tsawo mita 1 yayin da ake cikin layi. Ya zuwa yanzu, kashi 90% na wurare masu yawon bude ido a cikin kasar Sin sun fara yin rajista ta Intanet, matakin da ya yi amfani wajen kayyade yawan masu yawon bude ido dake son kaiwa ziyara a mataki-mataki. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China